Yaki da Yunwa: Gwamna Ya Gayyato 'Yan China domin Koyar da Noman Zamani

Yaki da Yunwa: Gwamna Ya Gayyato 'Yan China domin Koyar da Noman Zamani

  • Gwamna Umar Namadi ya rattaba hannu kan yarjejeniyar noma tare da kamfanin China CAMC da Hukumar Raya Noma ta Kasa
  • Yarjejeniyar za ta kawo sauye-sauye a harkar noma, tare da tallafawa manoma wajen amfani da kayan zamani a jihar Jigawa
  • Gwamna Umar Namadi ya bayyana cewa hakan na cikin matakan da yake dauka wajen raya jihar JIgawa da hakaba tattalinta

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - Gwamnan Jigawa, Umar Namadi ya jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniya tsakanin jihar, kamfanin China CAMC Engineering da Hukumar Raya Noma ta Kasa (NADF).

An gudanar da bikin sanya hannun a Beijing, kasar Sin, wanda ke zama wani babban mataki domin inganta harkokin noma a jihar Jigawa.

Jigawa
Gwamnatin Jigawa ta yi yarjejeniyar noma da kamfanin China. Hoto: Umar Namadi
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka rattaba hannu a kan yarjejeniyar ne a cikin wani sako da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

An cafke jigon NNPP kan zargin sukar gwamna Zulum, ana fargabar kai shi kotu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin inganta noma a jihar Jigawa

A karkashin yarjejeniyar, za a kawo ingantattun iri, tsarin ban ruwa na zamani, da kuma horo ga manoma domin noman ridi, waken suya da zobo.

Haka zalika, za a samar da kayan aiki na zamani domin tsaftacewa, busarwa, da sarrafa amfanin gona domin yin kafada da kafada da sauran kasahen duniya.

Shirin ya tanadi amfani da makamashi kamar hasken rana da iskar gas domin samar da wutar lantarki ga tsarin ban ruwa da cibiyoyin sarrafa amfanin gona..

Gina tattalin arzikin Jigawa da noman zamani

Gwamna Namadi ya bayyana cewa wannan shiri ba wai harkar noma kawai ya shafa ba, har ma da gina tattalin arzikin jihar Jigawa.

Yarjejeniyar za ta ba manoma damar samun kayan aiki da kudi domin bunkasa kasuwancinsu tare da bude hanyoyin kasuwanci na cikin gida da na kasashen duniya.

An fara raba tallafin noman Tinubu

Kara karanta wannan

Gwamna ya rasa kwamishinoni a ofis yayin ziyarar ba zata, ya yi gargadi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta fara rabon kayan tallafin noma a Najeriya inda aka fara rabo a wasu jihohi.

Ma'aikatar noma ta kasa ta bayyana cewa a karon farko manoma kimanin 6,000 ne za a ba tallafin noman alkama a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng