Yadda Lantarki Ta Babbaka Barawon Kayan Wuta Yana Tsaka da Sata
- Wani mutum da ake zargi da yunkurin satar wayar lantarki ya mutu bayan wuta ta kama shi a yankin Nsukka na Jihar Enugu
- Rahotanni sun nuna cewa mutumin ya zo wajen tare da wasu abokan cin mushensa, amma sun gudu bayan hadarin ya faru
- An yi bincike a cikin motar da suka zo da ita wajen satar bayan sun gudu sun bar ta kuma an samu kati dauke da bayanai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Enugu - Wani mutum ya rasa ransa a daren Litinin yayin yunkurin satar wayoyin lantarki a makarantar Firamare ta Ihe, karamar hukumar Nsukka, Jihar Enugu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mutumin yana kokarin satar wayoyin ƙarfe na lantarki mallakin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Enugu (EEDC).
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa mutumin da ake zargin ya je wajen satar ne tare da wasu gungun mutane.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barawon kayan lantarki ya mutu
Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa mutumin da ake zargi ya je satar ya mutu bayan wuta ta kama shi yana kokarin cire wayoyin lantarki.
Rahotanni sun ce gawar mamacin ta nuna alamun ƙonewa sosai a jikinsa, alamar da ke nuna karfin wutar da ya gamu da ita.
Masu satar kayan wuta sun gudu
An gano cewa mutumin ya zo tare da wasu mutane a cikin wata ƙaramar mota mai lambar rajista BLF-203XA.
Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin na faruwa sauran abokan nasa suka barshi a wurin suka gudu domin tsira da rayukansu.
Wani ganau ya bayyana cewa bayan da aka binciki motar da suka bari, an samu wani katin shaida a cikinta wanda ake zargin zai iya taimakawa wajen gano mutumin.
An kama barawon kayan lantarkin masallaci
A wani rahoton, kun ji cewa jami'an NSCDC sun kama wani mutum da ake zargi da satar kayan wuta a masallacin Juma'a a jihar Kano.
Rahoton Legit ya nuna an kama mutumin ne yayin da ya yi yunkurin sayar da kayan wutar a kasuwa, ya kuma shaida cewa ya saba sata a masallacin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng