Gwamna a Najeriya Ya Gwangwaje Kowane Ma'aikaci da Ɗan Fansho da Kyautar N100,000
- Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya ba da umarnin turawa kowane ma'aikaci alawus na N100,000 albarkacin bikin kirismeti
- Fubara ya amince a bai wa ƴan fansho kyautar wannan kudi daidai da ma'aikata duk domin su yi shagulgulan kirismeti cikin walwala
- Shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Ribas ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a yammacin yau Talata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya gwangwaje ma'aikata da ƴan fansho da kyautar N100,000 domin shagulgulan kirismetin bana 2024.
Gwamna Fubara ya amince a turawa kowane ma'aikaci da ɗan fansho waɗannan kuɗi domin su yi bukukuwar kirismeti da sabuwar shekara cikin walwala.
Shugaban ma'aikatan gwamnatin Ribas, Dr. George Nweke ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar ranar Talata, kamar yadda Leadership ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Fubara ya jiƙa ma'aikata da kuɗi
Ya ce ma'aikatan gwamnati a kowace ma'aikata da hukumomin gwamnati za su samu wannan kyauta ta kirismeti nan ba da jimawa ba.
"Ina farin cikin sanar da al'umma cewa gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya amince a ba kowane ma'aikacin gwamnati da ƴan fansho kyautar N100,000 domin shagalin kirismeti."
"Ma'aikata a dukkan hukumomi da ma'aikatun gwamnatin Ribas za su ci gajiyar wannan alawus na kirisnetin bana 2024.
"Mai girma gwamna ya rattaɓa hannu a ba da alawus din ranar 23 ga watan Disamba kuma ya ba da umarnin a fara turawa ma'aikata kuɗin nan take."
Gwamna ya maimaita abin da ya yi bara
Dr. Nweke ya ce wannan shi ne karo na biyu da gwamnan ya gwangwaje ma'aikata da alawus na N100,000 domin su sha shagalin kirismeti cikin farin ciki.
Shugaban ma'aikatan ya ce adadin kuɗin ya zarce mafi ƙarancin albashin da ake biyan ma'aikatan gwamnati a Najeriya.
An fara biyan sabon albashin N85,000
A wani labarin kun ji cewa gwamnatin jihar Ribas ta fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N85,000 a karshen wstan Nuwamba.
Gwamnan ya cika alƙawarin da ya ɗauka kuma ma'aiƙata sun yaba da ganin sabon albashin a cikin asusun bankunansu.
Asali: Legit.ng