'Yan Sanda Sun Yi Kazamin Artabu da 'Yan Bindiga, Rayuka Sun Salwanta

'Yan Sanda Sun Yi Kazamin Artabu da 'Yan Bindiga, Rayuka Sun Salwanta

  • Jami'an rundunar ƴan sanda sun yi arangama da ƴan bindiga a jihar Imo da ke yankin Kudu maso Gabas na Najeriya
  • Ƴan sandan sun sheƙe mutum uku daga cikin ƴan bindigan waɗanda ake zargin ƴan ƙungiyar IPOB ne
  • Kakakin ƴan sandan Imo, ya bayyana cewa wasu jami'an rundunar guda biyu sun rasu bayan sun samu raunuka yayin fafatawar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Imo - Rundunar ƴan sandan jihar Imo da ke yaƙi da masu garkuwa da mutane ta yi nasarar kashe wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan ƙungiyar IPOB ne.

Ƴan sandan sun hallaka ƴan bindigan ne a wani artabu da suka yi a garin Orogwe da ke ƙaramar hukumar Owerri ta Yamma a ranar, 19 ga watan Disamban 2024.

'Yan sanda sun hallaka 'yan bindiga a Imo
'Yan sanda sun sheke 'yan bindiga a jihar Imo Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Imo, Henry Okoye, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Ana shirin Kirsimeti, yaran Bello Turji sun yi ta'asa a Sokoto

Sai dai, abin takaici jami’an ƴan sanda biyu sun rasa rayukansu a yayin musayar wutan da aka yi.

Yadda ƴan sanda suka kashe ƴan bindiga

Ƴan bindigan sun buɗe wuta ne bayan hango jami'an ƴan sanda, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku tare da cafke wasu mutum biyu.

Kakakin rundunar ƴan sandan ya tabbatar da cafke David Ifeanyichukwu mai shekara 20 da kuma Abuchi Joseph mai shekara 24. 

"Farmakin ƴan sanda wanda ya gudana a ranar 19 ga watan Disamba, 2024, a Orogwe, ƙaramar hukumar Owerri ta Yamma, ya biyo bayan samun bayanan sirri."
"A yayin arangamar ƴan sandan sun ƙwato bindigu ƙirar AK-47 guda shida, alburusai 131, bindigogi ƙirar gida da motoci guda biyu na sata."
"Abin takaici, jami’an ƴan sanda biyu sun samu raunuka a yayin musayar wuta kuma daga baya sun mutu."
"Rundunar ƴan sandan jihar Imo ta yi alhinin rashin da aka yi tare da yabawa ƙwazon da suka yi wajen gudanar da ayyukansu."

Kara karanta wannan

IGP ya umarci a rika dukan 'yan sanda da ke bincike a kan hanya? An gano gaskiya

- Henry Okoye

Tirela ta murƙushe ƴan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa kwanan nan wani hatsarin mota ya ritsa da jami'an rundunar ƴan sanda na reshen jihar Ondo.

Hatsarin wanda ya faru bayan motar tirela ta murƙushe ta ƴan sanda, ya yi sanadiyyar rasuwar jami'an tsaron guda uku.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng