"Babu Tausayi": Kusa a PDP Ya Caccaki Tinubu, Ya Fadi Halin da Ya Jefa 'Yan Najeriya

"Babu Tausayi": Kusa a PDP Ya Caccaki Tinubu, Ya Fadi Halin da Ya Jefa 'Yan Najeriya

  • Ƙusa a jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, Bode George ya caccaki shugaban ƙasa, mai girma Bola Ahmed Tinubu
  • Bode George ya bayyana cewa hirar da Tinubu ya yi da ƴan jarida ta nuna bai tausayin yunwa da talauci da ƴan Najeriya suke ciki
  • Ya buƙaci Tinubu da ya ba da tallafi ga mutanen da manufofin gwamnatinsa suka talauta tare da jefa su cikin mawuyacin hali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Jigo a jam'iyyar PDP, Bode George, ya caccaki shugaban ƙasa Bola Tinubu kan hirar da ya yi da ƴan jarida.

Bode George ya bayyana cewa kalaman shugaba Tinubu sun nuna cewa ba ya tausayin halin da ƴan Najeriya suka tsinsu kansu a ciki.

Bode George ya caccaki Tinubu
Bode George ya caccaki Shugaba Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Olabode George
Asali: Facebook

Jigon PDP ya taso Bola Tinubu a gaba

Bode George ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' a ranar Talata.

Kara karanta wannan

"Akwai kura kurai": Shugaba Tinubu ya tabo batun bincikar hafsoshin tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon na PDP ya bayyana cewa akwai yunwa a ƙasa amma shugaba Tinubu ya haƙiƙance cewa manufofinsa na aiki.

Jaridar Daily Trust wacce ta bibiyi hirar ta ce ɗan kwamitin amintattu na PDP ya bayyana cewa bai kamata a ce an kawo ƙarshen shekara da wannan hirar ta Tinubu ba.

Me Bode George ya ce kan Tinubu?

"Akwai yunwa da fushi a cikin ƙasa, amma shugaban ƙasa yana ci gaba da haƙiƙancewa cewa manufofinsa na aiki yayin da ƴan Najeriya da dama ke ƙara talaucewa sannan kasuwanci na durƙushewa."
"Mu ba mu ganin aikin da manufofin ke yi, abubuwa kullum ƙara taɓarɓarwa suke yi. Yunwa ba ruwanta da surutunka, ka yi abin da za a gani a ƙasa."
"Na yi mamakin cewa babu tausayi ko kaɗan a cikin tattaunawar. Meyasa aka yi tattaunawar tun da farko."

- Bode George

Bode George wanda ya haƙiƙance a rage farashin man fetur, ya buƙaci Tinubu ya samar da tallafi ga ƴan Najeriyan da manufofin gwamnatinsa suka jefa su cikin yunwa.

Kara karanta wannan

2027: APC ta fadi abin da zai sa Tinubu ya lashe kuri'un Arewa ta Tsakiya

Tinubu ya magantu kan bincikar hafsun tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi tsokaci kan batun bincikar hafsoshin tsaron Najeriya.

Mai girma Bola Tinubu ya nuna cewa ya gamsu da kamun ludayinsu domin haka babu buƙatar ya binciki yadda suke kashe kuɗaɗe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng