Gwamna Ya Rage Matsalar Rashin Aikin yi, Ya Dauki Ma'aikata kusan 500

Gwamna Ya Rage Matsalar Rashin Aikin yi, Ya Dauki Ma'aikata kusan 500

  • Rahotanni na nuni da cewa gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya amince da daukar ma’aikatan lafiya 424
  • Gwamnatin Yobe ta dauki ma'aikatan jinya da ungozoma 205 da wasu kwararru 219 daga bangarorin lafiya daban-daban
  • Gwaman ya ce za a rarraba ma’aikatan zuwa yankunan karkara da birane domin samar da ingantacciyar kula da lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum..

Jihar Yobe - Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da daukar ma’aikatan lafiya guda 424 domin karfafa aikin kiwon lafiya a fadin jihar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an dauki masu yawa daga cikin ma'aikatan ne bayan kammala karatu a makarantun jihar.

Mala buni
Mai Mala Buni ya dauki ma'aikatan lafiya a Yobe. Hoto: Mamman Mohammed
Asali: Facebook

Daraktan Yada Labaran Gwamna Buni, Mamman Mohammed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamna ya rasa kwamishinoni a ofis yayin ziyarar ba zata, ya yi gargadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mamman Mohammed ya ce matakin ya dace da manufar gwamnati na samar da ingantacciyar kula da lafiya ga jama’a.

Za a rarraba ma'aikatan lafiya a jihar Yobe

Gwamna Buni ya dauki ma’aikata 205 tsakanin ungozoma da masu jinya da kuma kwararru 219 a bangarori daban-daban domin cike gibin ma’aikatan lafiya a jihar.

Sanarwar gwamnatin ta ce za a rarraba ma’aikatan zuwa manyan asibitoci da kananan cibiyoyin lafiya a yankunan karkara da birane.

Gwamna Buni ya nanata cewa daukar ma’aikatan na daga cikin manufofin gwamnatinsa na inganta kiwon lafiya.

Buni zai cigaba da kula da harkar lafiya

Gwamnan ya bayyana cewa kula da lafiya na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ke ba muhimmanci.

Ya yi alkawarin ci gaba da samar da kayayyakin aikin zamani, kayan aikin likitoci, da ma’aikata masu kwarewa domin bunkasa kiwon lafiya a jihar.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin jihar Yobe za ta ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren da za su tabbatar da ingantacciyar kula da lafiyar jama’a.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta ya ƙara tsananta, gwamna ya fusata, ya soke naɗin sabon sarki

An kafa ma'ikatar dabbobi a jihar Yobe

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Yobe ta kafa ma'aikatar kula da dabbobi domin habaka harkar kiwo.

Gwamna Mai Mala Buni ya yi koyi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne wajen kafa ma'aikatar kamar yadda aka yi a matakin kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng