Rikicin Sarauta Ya Ƙara Tsananta, Gwamna Ya Fusata, Ya Soke Naɗin Sabon Sarki
- Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya sa baki a rikicin sarautar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a garin Oba da ke ƙaramar hukumar Idemili
- Soludo ya ɗauki zafi kan lamarin, ya ba da umarnin dakatar da zaɓen sabon sarkin kuma ya sa jami'an tsaro su kama duk wanda ya yi kunnen ƙashi
- Mai girma gwamna ya ce har yanzun akwai shari'a a gaban kotu kan sarautar, don haka har zuwa lokacin da za a warware, garin zai zauna a haka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Anambra - Rikicin sarauta ya kara kamari a yankin Oba da ke ƙaramar hukumar Idemili a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.
Gwamnan Anambra, Farfesa Charles Soludo ya tsoma baki kan rikicin, ya ba da umarnin dakatar da naɗin sarkin Oba (Igwe na Oba) har sai baba ta gani.
Gwamna Soludo ya ɗauki tsattsauran mataki
Gwamnan ya kuma umarci rundunar ƴan sandan ta jihar ta cafke duk wanda ya fito yana ayyana kansa a matsayin Sarki a ƙaramar hukumar Idemili.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar mai girma gwamnan, babu wani zabe da aka gudanar a tsakanin al’umma domin naɗa sabon Igwe na Oba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Farfesa Soludo ya ce duk wani matakin naɗa sabon sarki da al'ummar garin Oba suka ɗauka bai halatta ba kuma laifi ne babba.
Kwamishinan ƙananan hukumomi da al’amuran garuruwa na jihar Anambra, Cif Tony Collins Nwabunwanne ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Rikicin sarautar ya kai gaban kotu
Ya kuma bayyana cewa akwai shari’ar da ke gaban kotu game da zaben sabon sarkin gargajiya na garin kuma har yanzu ba a ƙarƙare ta ba, rahoton Daily Post.
A sanarwar, Gwamna Soludo ya tabbatar da cewa daga nan har lokacin da za a warware wannan rikici na sarauta, garin Oba zai ci gaba da zama babu sarki.
Gwamna Soludo zai yi wa miyagu afuwa
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Charles Soludo ya ce a shirye yake ya yiwa dukkan miyagun da suka tuba su ajiye makamansu afuwa a jihar Anambra.
Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne da nufin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabi jihar da ke Kudancin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng