"Ba Abin da Za a Fasa," Bola Tinubu Ya Sake Magana Mai Ɗumi kan Kudirin Haraji

"Ba Abin da Za a Fasa," Bola Tinubu Ya Sake Magana Mai Ɗumi kan Kudirin Haraji

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa ba gudu ba ja da baya, batun sauya fasalin haraji na nan daram babu fashi
  • Mai girma Bola Tinubu ya ce ba dole ba ne sai kowa ya amince da kudirin harajin amma dai babu abin da za a fasa
  • Tinubu ya kuma buɗe kofar tattaunawa inda ya ce batun haraji yana bukatar a tafka muhawara kuma a hau teburin sulhu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa ba gudu ba ja da baya a shirinsa na sauya fasalin harajin Najeriya.

Bola Tinubu ya ce kudirorin canza fasalin harajin wanda gwamnatinsa ta ɓullo da su suna nan daram kuma babu fashi.

Shugaba Tinubu.
Bola Tinubu ya ce kudirin sake fasalin haraji na nan daram Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a tattaunawar da ya yi ƴan jarida karon farko tun bayan hawannsa mulki wanda NTA ta watsa mai tsaye.

Kara karanta wannan

"50 sun yi yawa": Bola Tinubu ya yi bayani kan yiwuwar ya sake korar wasu ministoci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kudirin harajin Tinubu ya tada kura

Kudirin sake fasalin haraji da ke gaban majalisar dokokin kasar nan ya haifar da cece-kuce tare da shan suka musamman daga shugabannin Arewa.

Hakan dai ya sa ƴan Majalisar Tarayya suka jingine batun, inda suka nemi sake tattaunawa kan kudirorin harajin.

Da yake jawabi kan kudirorin, Bola Tinubu ya ce ba dole kowa ya yi na'am da sake fasalin harajin ba amma dai babu fashi.

Tinubu ya ce sake fasalin haraji zama daram

"Sake fasalin haraji babu fashi, gyaran na talakawa ne kuma zai kara faɗaɗa hanyoyin samun haraji ta yadda za a samu ƙarin mutane masu biyan haraji.
"Alamar shugaba na gari shi ne ya yi abin da ya dace a lokacin da ya dace a yi shi."

Bola Tinubu ya buɗe kofar sake tattaunawa

Sai dai duba da yadda gwamnoni da sanatoci suke adawa da kudirin, Shugaba Tinubu ya ce a shirye yake a sake zama don tattaunawa kan batun.

Kara karanta wannan

"Mun samu nasara:" Sanata Ndume ya fadi amfanin watsi da kudirin harajin Tinubu

"Haraji wani batu ne da ke bukatar a yi muhawara kuma a zauna a tattauna, ba zan damu ba, a shirye nake a zauna kan lamarin"

Akpabio ya ba Tinubu tabbaci kan kudirin haraji

Kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya ba Tinubu tabbacin cewa ba za su baro kudirin ya mutu ba, za su zartar da shi.

Akpabio ya yi wannan magana ne a lokacin da yake jawabi yayin gabatar da kasafin kuɗin 2025, ya ce masu sukar kudirin ba su fahimce shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262