"Babu Lokaci": Zulum Ya Tunatar da Gwamnatin Tinubu Aikin da Za Ta Yi a Borno
- Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi magana kan gyara madatsar ruwan Alau da ta ɓalle
- Farfesa Zulum ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta gyara madatsar ruwan domin damina na ta ƙara matsowa a Najeriya
- Gwammnan ya bayyyana cewa tun da wuri ya kamata a yi gyaran domin gujewa sake aukuwar ambaliyar bana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya tunatar da gwamnatin tarayya dangane da gyara madatsar ruwa ta Alau.
Gwamna Babagana Zulum ya bayyana cewa saura wata huɗu damina ta dawo, inda ya buƙaci gwamnatin tarayya ta waiwayi gyaran madatsar ruwan wacce ta yi ambaliya a daminar bana.
Gwamna Zulum ya yi wannan roƙo ne a ranar Litinin yayin da yake karɓar cikakken rahoto daga kwamitin da ya binciki musabbabin rugujewar madatsar ruwan a Maiduguri, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane kira Zulum ya yi ga gwamnatin tarayya?
Gwamnan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta sake gina madatsar ruwan ta Alau, wacce ɓallewarta ta haddasa mummunar ambaliyar ruwa a garuruwan Maiduguri da Jere.
"A mako mai zuwa, za mu shiga watan Janairu, kuma za a yi ruwan sama a wasu sassan jihar Borno a watan Maris. Muna da ƙarancin lokaci!"
"Zai fi yi mana kyau idan muka fara abubuwa da wuri. Tawagar gwamnatin tarayya ta zo Maiduguri, kuma sun tattauna da kwamitin da muka ƙaddamar."
"A namu ɓangaren a matsayinmu na gwamnatin jiha, za mu yi iya bakin ƙoƙarinmu domin ganin mun kai wannan lamarin duk inda ya dace."
"Ina ganin cewa nan da ƴan kwanaki idan ba a yi wani aiki a ƙasa ba, zan je wurin mai girma shugaban ƙasa, na roƙe shi da ya bari hukumar raya yankin Arewa maso Gabas ta karɓe ragamar aikin sake ginawar nan take."
- Gwamna Babagana Umara Zulum
Gwamna Zulum ya samar da motoci
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi wa baƙi mazauna jihar Borno babban gata.
Gwamna Zulum ya samar da motoci kyauta waɗanda za su yi jigilar baƙi mazauna jihar da za su koma jihohinsu domin bukukuwan Kirsimeti.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng