Yadda Gwamnatin Tinubu Ta Shirya Rabon Tallafin N25,000 ga Magidanta Miliyan 15

Yadda Gwamnatin Tinubu Ta Shirya Rabon Tallafin N25,000 ga Magidanta Miliyan 15

  • Ministan jin kai da yaƙi da fatara, Nentawe Yilwatda ya ce gwamnatin Bola Tinubu za ta taimaki rayuwar ƴan Najeriya Miliyan 75
  • Yilwatda ya ce gwamnatin za ta rabawa magidanta miliyan 15 tallafin N25,000 na tsawon watanni uku a shekara ɗaya
  • Ya ce kamar yadda aka tsara, shirin tallafin zai zaƙulo magidanta ne kaɗai musamman mata saboda su ke kula da ƙananan yara a gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ministan harkokin jin kai da walwalar al'umma, Nentawe Yilwatda ya ce gwamnatin tarayya za ta bai wa magidanta miliyan 15 tallafin N25,000.

Ministan ya ce magidanta miliyan 15 da mutane miliyan 75 aka tsara za su ci gajiyar shirin tallafin tsabar kuɗi na CCT.

Ministan jin kai, Yilwatda.
Gwamnatin tarayya na shirin tallafawa mutum miliyan 75 da N25,000 Hoto: Nentawe Yilwatda
Asali: Twitter

A cewarsa, za a biya kowane magidanci ₦25,000 duk wata sau uku a shekara, kamar yadda tashar Channels tv ta kawo.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya ziyarci mutanen da aka ceto a hannun 'yan bindiga, ya ba da tallafi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu na tausayin talaka

Yilwatda ya ce matakin wani bangare ne a yunƙurin shugaba Bola Tinubu na rage raɗaɗin matsin tattalin arzikin da ƴan Najeriya ke ciki.

Ministan ya ce:

"Shugaban kasa ya san halin da ake ciki, akwai tsare-tsaren da ya ɓullo da su domin sauƙaƙawa talakawa da magance matsin rayuwar da ake ciki.
"Na farko, ya umarci mu ɗauki magidanta miliyan 15 a rijistar zamankewa domin tallafa masu. Magidanta ba gwauraye ba, akalla mai iyalai mutum biyar.
"Idan ka duba magidanta miliyan 15 da mutane akalla biyar a ƙarƙashinsu, a jimilance shugaban ƙasa na fatan taimakawa rayuwar mutune miliyan 75 a tsarin tallafin kuɗin CCT.

Gwamnatin tarayya za ta ba mata fifiko

Ministan ya bayyana cewa zuwa yanzu gwamnatin tarayya ta tallafawa magidanta miliyan biyar kuma tana koƙarin tsaftace aikin don ya isa ga waɗanda suka cancanta.

Ya ƙara da cewa sun bai wa mata magidanta fifiko saboda su ne waɗanda ke kulawa da ƙananan yara a gida.

Kara karanta wannan

"N50,000 duk wata": Gwamna ya tuna da matasa, ya fara rabon miliyoyin Naira

Gwamnatin Tinubu ta ci bashin sama da N5trn

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta kuma runtumo bashin kuɗi sama da Naira tiriliyan 5 domin cike gibin kasafin kudin 2024.

Gwamnatin ta bayyana cewa ciwo bashin ya zama tilas saboda gibin da aka samu a kasafin sakamakon rashin isassun kuɗaɗen shiga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262