Sarki Ya Haura Ta Katanga yayin da Wasu Miyagu Suka Kai Farmaki Fadarsa
- Mai martaba Etsu Nupe Lokoja ya tsallake rijiya da baya yayin da wasu miyagu suka farmaki fadarsa da tsakar daren Asabar
- Maharan sun ƙona motar sarkin da wasu kayayyaki a fadar amma ba su yi nasarar cutar da shi ba, ya gudu ta katanga
- Sarkin ya buƙaci ƴan kabilar Nupe su kaucewa kai hari da sunan ramuwar gayya kuma su zauna lafiya su bari jami'an tsaro su yi aikinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - ‘Yan bindiga sun kai hari fadar Etsu Nupe Lokoja, Mai martaba Emmanuel Akamisoko Dauda-Shelika, wanda ake kira da Nyamkpa IV a karshen mako.
Maharan sun cinna wa motar wuta a lokacin da suka kai harin amma sarkin ya samu nasarar tsira ba tare da sun cutar da shi ba.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa miyagun sun farmaki fadar sarkin ne ranar Asabar, 21 ga watan Disamba, 2024 da misalin karfe 1:00 na tsakar dare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin ya yi mamakin kai hari fadarsa
Yayin da yake ba da labarin abin da ya faru, Etsu Lokoja Nyamkpa IV, ya ce harin ya ba shi mamaki.
Mai martaba Dauda-Shelika ya ce:
"Na ji ana buga mani ƙofa da karfi, na tashi na leƙa ta taga saboda na yi mamakin me ya faru da tsadar dare haka, kwatsam na hangi hayaki na tashi a motata bayan maharan sun banka mata wuta.
"Da na fahimci hari aka kawo fadata sai na fasa bude ƙofar na bi ta ƙofar sirri ta baya, na haura katanga domin tsira da rayuwata."
Sarkin ya kara da cewa duk da kokarin da makwabtansa suka yi sai da wutar ta kona motarsa ƙurmus tare da da sauran kayayyakin da ke cikin fadar.
Sarkin ya bukaci a hukunta maharan
Basaraken ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su binciki lamarin tare da hukunta wadanda suka kai harin da masu daukar nauyinsu, rahoton Punch.
Mai martaba Dauda-Shelika ya bukaci ‘yan kabilar Nupe da ke Lokoja su guji duk wani nau’in harin ramuwar gayya, inda ya shawarce su da su zauna zaman lafiya.
Yan sanda sun cafke masu garkuwa
A wani rahoton, kun ji cewa wazu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun shiga hannun jami'an tsaro a jihar Kogi.
Dakarun ƴan sanda tare da taimakon wasu jami'an tsaro ƴan sakai sun kama ƴan bindigar tare da ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng