IGP Ya Umarci a Rika Dukan 'Yan Sanda da Ke Bincike a kan Hanya? An Gano Gaskiya
- Wasu rahotanni sun yaɗu masu nuna cewa shugaban ƴan sanda, ya umarci a riƙa dukan jami'an da ke bincike a kan hanya
- A makon nan, Rundunar ƴan sandan Najeriya ta fito ta yi martani inda ta bayyana hakan a matsayin ƙarya tsagwaronta
- Kakakin rundunar ya bayyana cewa IGP Egbetokun bai taɓa nuna goyon baya kan a ci zarafin jami'an tsaro ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Rundunar ƴan sandan Najeriya ta yi martani kan batun cewa IGP Kayode Egbetokun, ya umarci a riƙa dukan jami'an da ke bincike a kan hanyoyi.
Rundunar ƴan sanda ta ce Egbetokun bai umarci ƴan Najeriya da su riƙa lakaɗawa jami’an duka ba, a lokacin da suke gudanar da bincike.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa kakakin rundunar ƴan sandan, Muyiwa Adejobi, ya sanya a shafin X na hukumar a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ƴan sanda suka ce kan dukan jami'an tsaro?
Ya bayyana cewa shugaban ƴan sandan bai taɓa ba da goyon baya ba, kan a ci zarafin jami’an tsaro ba.
Muyiwa Adejobi ya ce labarin babu ƙamshin gaskiya a cikinsa, kuma ƙarya ce tsantsagwaronta.
"Rundunar ƴan sandan Najeriya na son yin magana kan wani labari na bogi da ya ɓullo, mai cewa IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya umarci mutane da su riƙa yi duka da jefa duwatsu ga jami’an ƴan sanda da ke neman bincikar wayoyinsu."
"Wannan iƙirarin gaba ɗayansa ƙarya ce kuma ba ta da madogara. IGP bai bayar da irin wannan umarnin da ke ƙarfafa cin zarafin jami’an tsaro ba."
"Maimakon haka, ya yi kira ga jama'a da su kai rahoton rashin ɗa'ar ƴan sanda ta hanyoyin da suka dace."
- Muyiwa Adejobi
Jami'an ƴan sanda sun tsallake cin hanci
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu jami'an ƴan sandan Najeriya sun tsallake tayin cin hancin N66m da wasu masu suka yi musu a jihae Legas.
Waɗanda ake zargin da suka ƙware wajen yin jabun satifiket sun yi tayin cin hancin ne bayan jami'an ƴan sanda sun cafke su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng