Shugaban APC, Ganduje Ya Bayyana Shirinsu a kan 'Yan Najeriya

Shugaban APC, Ganduje Ya Bayyana Shirinsu a kan 'Yan Najeriya

  • Shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa gwamnatinsu ta zo da shirin ingantawa jama'ar kasa
  • Ganduje ya fadi haka ne a Enugu yayin kaddamar da wata cibiyar a kan makamashi a jami'ar Nsukka da tallafin Bankin Duniya
  • Ya shaidawa 'yan kasa cewa akwai shirin da gwamnatin tarayya ta yi domin tabbatar da wadatar wutar lantarki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Enugu - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje, ya jaddada kudirin jam’iyyarsa na tabbatar da wadatar wutar lantarki ga gidaje da masana’antu.

Shugaban Jam’iyyar na Kasa ya bayyana wannan matsayin a matsayin muhimmin ginshiƙi don ci gaban tattalin arziki da jin daɗin ‘yan Najeriya.

Tinubu
Shugaban APC ya ce gwamnati za ta kyautata rayuwar jama'a Hoto: Bayo Onanuga/Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Vanguard ta ruwaito cewa Ganduje yayin bikin ƙaddamar da ginin cibiyar Africa Centre of Excellence for Sustainable Power and Energy Development da tallafin Bankin Duniya a Nsukka.

Kara karanta wannan

Yunwa: PDP ta alakanta turmutsitsin da ya hallaka jama'a da manufofin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya fadi shirin Tinubu ga ‘yan kasa

Jaridar The Sun ta wallafa cewa Dr. Ganduje, wanda tsohon gwamnan Zamfara, Alhaji Aliyu Shinkafi, ya wakilta, ya jaddada muhimmancin wutar lantarki wajen ci gaban kasa.

“Shirin ci gaban kasa yana inganta a karkashin gwamnatin shugaba Bola Tinubu, inda wutar lantarki ke zama ginshiƙi wajen samar da ci gaban ɗan adam da tattalin arziki mai ɗorewa,” in ji shi."

Ganduje ya yaba da samun tallafin Bankin Duniya

Dr. Abdullahi Ganduje ya yaba wa shugaban cibiyar, Farfesa Emenike Ejiogu, bisa samun tallafin Bankin Duniya.

Ya bayyana cewa Farfesa Ejiogu ne ya jagoranci ƙungiyar da ta samu tallafin $6m ga cibiyar, tare da ƙarin tallafin da ya haura $500,000 domin gudanar da gagarumin aikin.

“Ina yaba wa hangen nesa da ƙwarewar shugabanci na musamman da Farfesa Ejiogu ya nuna.
"Ayyuka irin waɗannan suna da matuƙar muhimmanci wajen sake daidaita matsayar ƙasarmu don inganta rayuwar ‘yan ƙasa,” in ji Ganduje.

Kara karanta wannan

Emefiele: Tsohon gwamnan CBN ya sake shiga matsala, kotu ta yi hukunci

APC ta yi watsi rahoton korar Ganduje

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyya mai mulki ta APC ta karyata rahoton da ke cewa akwai shirye-shiryen da aka yi wajen korar shugabanta, Abdullahi Ganduje.

Martanin na zuwa ne bayan labarun cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya shirya naɗa Ganduje a matsayin jakada, domin ya samu sauƙin tsige daga matsayinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.