NDLEA Ta Yi Babban Kamu, Ta Cafke Kayan Laifi Mafi Girma a Kano
- Jami'an hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA), sun yi babban kamu a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano
- Masu yaƙi da safarar ƙwayoyin sun cafke wani ɗan kasuwa ɗauke da hodar iblis mai nauyin kilogiram shida wacce ya yi yunƙurin shigo da ita Najeriya
- Kakakin NDLEA ya bayyana cewa kamen da aka yi, shi ne mafi girma tun lokacin da aka kafa ofishin hukumar a tashar filin jirgin saman
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Jami’an hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) sun dakile yunƙurin wani ɗan kasuwa mai suna Olisaka Chibuzo Calistus na safarar hodar ibilis guda 256.
Jami'an na NDLEA sun cafke ɗan kasuwan ne ɗauke da hodar iblis wacce nauyinta ya kai kilogiram shida a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano (MAKIA), da ke Kano.
An cafke hodar iblis a Kano
Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka sanya a shafin yanar gizo na ndlea.gov.org
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamen wanda shi ne mafi girma da aka taɓa yi na hodar iblis a filin jirgin saman na Kano tun bayan kafa ofishin NDLEA a shekarar 2006, an yi shi ne a ranar Lahadi 15 ga watan Disamba, 2024
An cafke ɗan kasuwan ne a lokacin da ake duba fasinjojin da ke cikin jirgin Ethiopian Airlines ET 941 wanda ya taso daga birnin Abidjan na Cote d'Ivoire bayan ya biyo ta birnin Addis Ababa, Habasha.
Femi Babafemi ya ce Olisaka, wanda ya yi iƙirarin cewa yana sana’ar shigowa da fitar da kayayyaki, an gano hodar ne a jikinsa bayan an duba shi.
NDLEA ta yi kamu a Legas
Kakakin na NDLEA ya kuma bayyana cewa jami'an hukumar sun daƙile wani yunƙurin da wani mai suna Olanrewaju Bada Akorede ya yi na fitar da wata ƙwaya ta rohypnol zuwa ƙasar Afirka ta Kudu.
Ya ce ya yi yunƙurin safarar ƙwayar ne ta filin jirgin sama na Murtala Muhammed International Airport (MMIA) Ikeja Legas.
Femi ya bayyana cewa an ɓoye ƙwayar ne a cikin wasu kaya ɗauke da kwaki, takalma, singileti ta maza da sauran kayayyaki.
NDLEA ta cafke ƙwayoyi
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an hukumar NDLEA sun cafke wasu ƙwayoyi da aka yi yunƙurin yin safararsu zuwa ƙasar waje.
Jami'an na NDLEA sun cafke ƙwayoyin ne waɗanda aka ɓoye su a cikin buhunan gyada da aya domin fitar da su zuwa ƙasar Burtaniya.
Asali: Legit.ng