Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwa, Ta Lakume Shaguna Masu Yawa

Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwa, Ta Lakume Shaguna Masu Yawa

  • Gobara ta yi ɓarna bayan ta tashi a wata fitacciyar kasuwa da ke birnin Gusau a jihar Zamfara a yankin Arewa maso Yamma
  • Lamarin wanda ya auku a yammacin ranar Asabar ya jawo shaguna da dama sun ƙone a kasuwar wacce ta yi fice wurin sayar da babura da kayan gyara
  • Jami'an ba da agajin gaggawa daga hukumar kashe gobara ta Zamfara sun garzaya zuwa kasuwar inda suka yi ƙoƙarin hana yaɗuwarta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Wata gobara a jiya ta lakume kasuwar baburan ‘Yar-Dole da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Gobarar wacce ta tashi da yammacin ranar Asabar, ta yi ɓarna ga ƴan kasuwa da mazauna yankin inda shaguna da rumfuna da dama suka ƙone ƙurmus.

Gobara ta tashi a Zamfara
Gobara ta tashi a wata kasuwa a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Leadership ta rahoto cewa shaidun gani da ido sun ce gobarar ta bazu cikin sauri a kasuwar.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi da wata tankar mai ta tarwatse ana cikin jimamin rasa rayuka a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gobara ta laƙume shaguna a Zamfara

Kasuwar Yar Dole dai ta shahara wajen sayar da babura da kayayyakin gyara.

"Ba mu san musabbabin tashin gobarar ba, sai dai kawai mu ka ga wuta daga shagunan babura, amma hukumar kashe gobara na ci gaba da fafutukar kashe ta."

- Wata majiya

A wurin da lamarin ya faru, ana iya ganin yawancin ƴan kasuwa da masu shaguna suna ta ƙoƙarin ceto kayansu, amma ba su yi nasara ba, saboda zafin wutar da ta tashi.

Jami’an bayar da agajin gaggawa na hukumar kashe gobara ta jihar Zamfara sun isa wurin jim kadan bayan faruwar gobarar, inda suka ta ƙoƙarin kashe gobarar da hana ci gaba da yaɗuwarta.

Gobara ta yi ɓarna a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta yi bayanin irin ɓarnar da gobara ta yi a cikin watan Nuwamban 2024.

Kara karanta wannan

Sai a kiyaye: Gwamnan Kano ya fadi hukuncin da zai fara yiwa masu kin biyan haraji

Hukumar kashe gobarar ta bayyana cewa gobarar ta jawo asarar miliyoyin naira yayin da aka samu asarar rayukan mutane uku a lokuta daban-daban.

Hukumar ta kuma sanar da cewa ta samu nasarar ceto kayayyakin miliyoyin naira waɗanda gobarar ta so laƙumewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng