Kirsimeti: Gwamna Zulum Ya Yi Wa Mazauna Jihar Borno Babban Gata

Kirsimeti: Gwamna Zulum Ya Yi Wa Mazauna Jihar Borno Babban Gata

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi wa baƙi mazauna jihar gata domin komawa jihohinsu
  • Zulum ya samar da motoci kyauta da za su yi jigilar mutane 710 zuwa jihohinsu domin gudanar da bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara
  • Baya samar musu da motocin da za su yi jigilarsu kyauta, Gwamnan ya kuma ba kowannensu kuɗi N50,000

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya samar da motocin da za su yi jigila kyauta ga mutane 710 da ba ƴan asalin jihar ba.

Gwamna Zulum ya samar motocin ne, domin ba su damar zuwa jihohinsu gudanar da bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara tare da ƴan uwansu.

Zulum ya samar da motoci kyauta
Gwamna Zulum ya samar da motocin da za su yi jigilar baki kyauta Hoto: @ProfZulum
Asali: Facebook

Gwamna Zulum ya samar da motoci kyauta

Shirin samar da motocin kyauta wanda aka ƙaddamar a ranar Asabar a tashar Borno Express Bus Terminus, ya fara da mutane 285 waɗanda za su yi tafiya zuwa sassa daban-daban na ƙasar nan, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Karyar ƴan bindiga da sauran miyagu ta kare a Najeriya, sanata ya hango shirin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kashi na biyu na mutane 285 za su yi tafiya a ranar Lahadi, yayin da sauran za su bar a jihar a ranar Litinin.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da shirin, shugaban ƙungiyar Ohanaeze APC Support Group, Cif Ugochukwu Egwidike, ya ce kowane daga cikin mutane 710, baya ga jigilarsu kyauta, za a ba su kuɗi N50,000.

Ya bayyana cewa zawarawa kusan 250 da ba za su yi tafiya ba, za a ba kowannensu Naira 50,000 domin bikin Kirsimeti.

Egwudike ya ƙara da cewa Gwamna Zulum ya samar da gagarumin ci gaba wajen tallafawa mabuƙata da tsare-tsare daban-daban da nufin rage raɗaɗin talauci da inganta walwalar jama’a.

Gwamna Zulum ya samu nasara a fannin ilmi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa ya samu nasarar rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya tafi hutu bayan gabatar da kasafin kudin 2025

Gwamna Zulum ya kuma bayyana cewa a cikin shekara biyar da ya kwashe a mulkin jihar Borno, ya samar da ci gaba mai yawa a fannin ilmi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng