Matatar Ɗangote Za Ta Fara Sayar Fetur ga Ƴan Najeriya, Ta Faɗi Sabon Farashin Lita

Matatar Ɗangote Za Ta Fara Sayar Fetur ga Ƴan Najeriya, Ta Faɗi Sabon Farashin Lita

  • Bayan ragin da ta yi wa ƴan kasuwa, matatar Ɗangote ta kulla yarjejeniya da kamfanin MRS domin fara sayar da fetur kai tsaye ga ƴan Najeriya
  • Matatar attajirin ɗan kasuwar ta bayyana cewa za ta fara sayar da fetur a gidajen man MRS kowace lita a farashin N935
  • Wannan dai na zuwa ne bayan kamfanin mai na ƙasa watau NNPCL ya sanar da rage farashin man feturinsa zuwa kimanin N899

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Matatar man Ɗangote ta yi haɗin guiwa da kamfanin mai na MRS domin fara sayar da man fetur a gidajen mai a faɗin ƙasar nan.

Matatar attajirin ɗan kasuwar ta sanar da cewa za ta fara sayar fetur kowace lita kan N935 a gidan mai na MRS da ke faɗin jihohin Najeriya.

Kara karanta wannan

Dangote: Farashin litar man fetur ya sauka a gidajen man ƴan kasuwa da NNPCL

Alhaji Aliko Ɗangote.
Matatar Ɗangote za ta fara sayar da fetur kai tsaye ga ƴan Najeriya a farashin N935 Hoto: Dangote Group
Asali: Getty Images

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da rukunin kamfanonin Ɗangote Group ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter yau Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matatar Ɗangote ta matso kusa da ƴan Najeriya

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kalilan bayan Ɗangote ya rage farashin feturi zuwa N899 ga ƴan kasuwa.

Hakan ya sa ƴan kasuwa suka fara sauke farashin litar mai duk da dai har yanzun bai dawo ƙasa da N1,000 ba amma sun ce a makon gobe za a ƙara ganin ragi.

A wani yunkuri na shigowa kasuwar fetur dumu-dumu, matatar Ɗangote ta ƙulla yarjejeniya da gidajen man MRS domin fara sayar ds fetur kai tsaye ga ƴan Najeriya.

Matatar Ɗangote ta Bayyana sabon farashi

A sanarwar da ta wallafa a shafin X, matatar Ɗangote ta ce:

“Don tabbatar da cewa ragin da muka yi ya kai ga ƴan Najeriya, mun kulla yarjejeniya da MRS don sayar da man fetur a gidajen mansu kowace lita N935.

Kara karanta wannan

Matatar Dangote ta yi bayanin 'rancen $1bn' da kamfanin NNPCL ya ba ta

"Yanzu haka mun riga nun fara sayarwa a wannan farashin a jihar Legas kuma daga nan zuwa ranar Litinin za mu fara kai kaya dukkan sassan ƙasar nan."

Kamfanin NNPCL ya rage farashin fetur

Rahoto ya gabata cewa kamfanin NNPCL ya bi sahun matatar Ɗangite, ya sanar da ragin farashin kowace litar man fetur daga N1,020 zuwa N899.

Wannan ragi da ake ci gaba da samu na zuwa ne a daidai lokacin da ake tunkarar bukukuwan kirismeti da sabuwar shekara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262