Gwamna Ya Fita Daban a Najeriya, Ya ba Ma'aikatan Gwamnati Hutun Kwanaki 7

Gwamna Ya Fita Daban a Najeriya, Ya ba Ma'aikatan Gwamnati Hutun Kwanaki 7

  • Gwamnan Bayelsa, Douye Diri ya ba ma'aikata hutun mako guda domin su yi shagulgulan kirismeti da sabuwar shekara a gida
  • Kwamishinar yaɗa labarai da wayar da kan jama'a ta jihar ta ce hutun zai fara ne daga ranar 24 zuwa 30 ga watan Disamba, 2024
  • Gwamna Diri ya taya ɗaukacin al'ummar Bayelsa murnar bikin kirismeti da sabuwar shekara tare da miƙa sakon fatan alheri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayelsa - Gwamna Douye Diri na Bayelsa ya amince da hutun Kirsimeti ga daukacin ma’aikatan gwamnati a jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinar yada labarai, wayar da kan jama’a da dabaru ta jihar, Misis Ebiuwou Koku-Obiyai ta fitar jiya Juma'a.

Gwamna Douye Diri.
Bayelsa: Gwamna Diri ya ba ma'aikata hutun kwanaki 7 saboda zuwan Kirismeti Hoto: Douye Diri
Asali: Facebook

Gwamna Diri ya ba da hutun kwanaki 7

Kwamishinar ta bayyana cewa hutun Kirismetin zai fara daga ranar 24 zuwa ranar 30 ga watan Disambar 2024, kamar yadda Vanguard ta kawo.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan MTN, ta ci tararsa N15m kan cire kudi babu ka'ida

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai Misis Ebiuwou ta ƙara da cewa muhimman ma'aikata kamar likitoci za su ci gaba da zuwa wurin aiki kamar yadda suka saba ma'ana ban da su a hutun.

A ranar 25 ga watan Disamba a kowace shekara mabiya addinin Kirista a Najeriya da sauran kasashen duniya ke bikin kirismeti.

Haka nan mako ɗaya bayan nan kuma ake bikin sabuwar shekara, wanda aka saba yi a tsakiyar daren 31 ga Disamba da farkon awannin 1 ga watan Janairu.

Gwamnan Bayelsa ya fita daban a bada hutu

Duk da gwamnatin tarayya ta saba bayar da hutun kwana biyu, Gwamna Bayelsa ya bai wa ma'aikatansa hutun mako guda su yi shagalinsu a gida.

A sanarwar da kwamishinar yaɗa labaran ta fitar, ta ce:

"Wannan hutun zai fara ne a ranar 24 ga Disamba kuma ya ƙare ranar 30 ga Disamba, 2024.
"Sannan an keɓe ma'aikata masu mahimmanci (kamar likitoci) daga wannan hutu kuma ana sa ran za su ci gaba da zuwa wurin aiki kamar yadda aka saba."

Kara karanta wannan

Kirsimeti: Gwamna a Arewa ya ware tirelolin shinkafa 100 domin rabawa al'umma

Gwamna Diri ya ƙara godewa mazauna Bayelsa bisa goyon bayan da suke ba shi tare da yi wa kowa fatan alheri da murnar Kirsimeti da sabuwar shekara.

Gwamna Diri ya yi magana kan siyasar Jonathan

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Bayelsa ya yi ikirarin cewa Goodluck Jonathan ne ya rusa masa burin siyasa tun farko.

Douye Diri ya ce tsarin da tsohon shugaban ƙasar ya ɓullo da shi ne ya shafe shi a siyasa kafin daga bisani ya samu nasarar tafiya Majalisar tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262