'Abu Ya Zo da Karar Kwana': Wani Jami'an Tsaro Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Bakin Aiki
- Rundunar ƴan sanda a jihar Ogun ta tabbatar da rasuwar wani jami'in tsaro, Kareem Hammed wanda ya faɗi a bakin aiki
- Mai magana da yawun rundunar, Omolola Odutola ta ce mamacin ya rasa ransa ne kwanaki kaɗan bayan ya yi jinyar zazzabin cizon sauro
- A halin yanzun ƴan sanda sun fara bincike kan lamarin, kuma sun kai gawar mamacin babban asibiti a yi bikcike a kanta
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ogun - Rundunar ‘yan sanda reshen a Ogun a ranar Alhamis ta tabbatar da mutuwar wani jami'in tsaro, Kareem Hammed, wanda ya yanke jiki ya fadi a wurin aiki.
Kareem Hammed ɗan kimanin shekaru 42 a duniya, yana aiki ne da kamfanin tsaro na Fortune da ke Onipanu a jihar Legas.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa mako guda da wuce aka sallamo marigayin daga asibiti bayan ya yi jinyar zazzaɓin cizon sauro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda jami'in tsaron ya mutu a wurin aiki
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Omolola Odutola, ta ce wani Adejumobi Adetunji, abokin aikin mamacin ne ya kai rahoton faruwar lamarin caji ofis na Odeda.
A cewar Odutola, marigayin ya fadi da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Laraba, kuma an garzaya da shi babban asibitin Odeda domin samun kulawar gaggawa.
Ta ce da misalin karfe 6:20 na safiyar ranar Alhamis, aka sanar da DPO na caji ofis ɗin Odeda cewa mutumin ya mutu, rahoton Daily Post.
Rundunar ƴan sanda ta fara bincike
“Wannan lamarin ya faru ne a ranar 18 ga watan Disamba, 2024, da misalin karfe 5:30 na yamma mako guda bayan an sallamo Kareem daga asibitin da ya yi jinyar zazzaɓi.
"An ɗauko shi bayan ya faɗi zuwa asibiti domin ya samu kulawar gaggawa amma daga baya likita ya tabbatar da rai ya yi halinsa washe garin ranar da abin ya faru.
- Omolola Odutola.
Kakakin ƴan sandar ta ce sun fara gudanar da bincike kan lamarin yayin da aka kai gawar mamacin babban asibitin Odeda domin a yi binciken gawa.
Yan sanda sun kama wata budurwa
A wani rahoton, kun ji 'yan sanda sun kama wata budurwa da ake zargin ta kashe ɗan gaba da fatiha da ta haifa wanda bai gama cika shekara ɗaya a duniya ba.
An ruwaito cewa budurwar ta hallaka jaririnta na ta ne saboda tsangwamar da aka fara nuna mata, daga baya ta shaidawa makusantanta cewa ya ɓata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

