Dangote: Farashin Litar Man Fetur Ya Sauka a Gidajen Man Ƴan Kasuwa da NNPCL

Dangote: Farashin Litar Man Fetur Ya Sauka a Gidajen Man Ƴan Kasuwa da NNPCL

  • Farashin litar man fetur ya fara raguwa a gidajen man NNPCL da na ƴan kasuwa bayan ragin da matatar Ɗangote ta yi
  • Mai magana da yawun kungiyar daillalan mai (IPMAN) ya ce zuwa makon gobe, mutane za su fara amfana da ragin litar man Ɗangote
  • Masana sun bayyana cewa wannan matakin zai farfaɗo da kwarin guiwar al'umma a halin ƙuncin da ake ciki a yau

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Rahotanni sun nuna cewa farashin litar man fetur ya fara sauka a gidajen man ƴan kasuwa da na kamfanin NNPCL a sassan Najeriya.

Hakan dai na da alaƙa da matakin matatar man feturin Ɗangote na rage farashin litar fetur saboda zuwan bukukuwan kirismeti da sabuwar shekara.

Gidan mai.
Farashin msn fetur ya fara sauka bayan ragin da matatar Ɗangote ta yi Hoto: NNPCL
Asali: Getty Images

Ɗangote ya rage farashin man fetur

Matatar Ɗangote ta sauke farashin kowace litar fetur zuwa N899.50 domin sauƙaƙawa ƴan Najeriya, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Matatar Dangote ta yi bayanin 'rancen $1bn' da kamfanin NNPCL ya ba ta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan wannan rangwamen, matatar Ɗangote ta bullo da garabasar ba kwastomomi bashin litar mai a duk lita guda da suka saya da tsabar kuɗi.

Yadda fetur ya fara sauka a gudajen mai

An ruwaito cewa kwanan nan kamfanin mai na kasa watau NNPCL ya rage farashin lita a gidajen mansa daga N1,025 zuwa N1,010 a jihar Legas.

Hakazalika, galibin manyan ‘yan kasuwa sun rage farashi a gidan mansu duk da cewa babu wanda ke siyar da lita ƙasa da N1,000 a halin yanzu.

Masana sun bayyana cewa wannan saukin da aka samu na ɗaya daga cikin amfanin tsame hannun gwamnati a harkokin yanke farashin man fetur.

A cewarsu, rage farashin da Ɗangote ya yi zai iya zama silar da man fetur zai sauka a Najeriya, rahoton Channels tv.

Tasirin ragin da matatar Ɗangoe ta yi

Mai magana da yawun kungiyar dillalan mai watau IPMAN, Alhaji Olanrewaju Okanlawon, ya ce nan da mako mai zuwa za a ga tasirin ragin da Ɗangote ya yi a gidajen mai.

Kara karanta wannan

Yan kasuwa sun sanar da samun saukin farashin litar fetur

Wani masanin harkokin makamshi, Dr. Ayodele Oni ya ce:

"Wannan ragin da aka yi zai dawo da ƙwarin guiwar jama'a game da matakin barin kasuwa ta riƙa yanke farashin mai."

NNPCL ya faɗi taimakon da ya yiwa Ɗangote

A wani labarin, kun ji cewa kamfanin mai na kasa watau NNPCL ya yi ikirarin cewa sai da ya runtumo bashin Dala biliyan 1 domin taimakawa matatar Ɗangote.

Kamfanin ya bayyana cewa ya yi iya bakin kokarinsa wajen ganin matatar attajirin ɗan kasuwar ta fara aiki a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262