Hajjin 2025: Hukumar NAHCON Ta Shirya Saukakawa Maniyyata

Hajjin 2025: Hukumar NAHCON Ta Shirya Saukakawa Maniyyata

  • Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta yi magana kan shirin soke amfani da Dala wajen biyan kuɗaden aikin Hajji
  • Shugaban hukumar NAHCON ya bayyana cewa daina amfani da Dala wajen biyan kuɗaden zai rage kuɗaɗen da maniyyata ke kashewa
  • Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya nuna godiyarsa ga gwamnatin tarayya kan tallafin da take bayarwa domin aikin Hajji

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Hukumar Alhazai ta ƙasa NAHCON ta bayyana shirin soke amfani da dala wajen biyan kudaden da suka shafi aikin Hajji.

Hukumar NAHCON ta bayyana cewa matakin, na da nufin rage tashin gwauron zaɓin da kuɗaɗe da ake kashewa wajen aikin Hajji ke yi.

NAHCON za ta daina amfani da Dala
Hukumar NAHCON za ta daina amfani da Dala wajen biyan kudin aikin Hajji Hoto: National Hajj Commission
Asali: Facebook

Shugaban hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Sarkin Argungu a fadarsa, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya kai matsalolin Najeriya gaban Allah, ya yi addu'ar samun ci gaba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NAHCON za ta daina amfani da Dala

Farfesa Abdullahi Saleh ya bayyana cewa biyan kuɗin abubuwan da suka shafi Hajji kamar kuɗin jirgi da Dala, ya taimaka matuƙa wajen sanyawa aikin Hajji ya yi tsada, wanda hakan ya sa ƴan Najeriya da dama ba su iya biya.

Shugaban hukumar ta NAHCON ya yabawa gwamnatin tarayya bisa tallafin da ta ke bayarwa musamman tallafin aikin Hajji.

Sai dai ya nuna damuwarsa kan yadda ake jinkirin biyan kuɗin aikin Hajji, lamarin da ya sa Najeriya ta gaza cike kason da aka ware mata na maniyyata, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Ya yi kira ga sarakunan gargajiya da shugabannin addini da su taimaka wajen kawar da amfani dala a harkokin da suka shafi aikin hajji ta hanyar tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

Maniyyata za su samu sauƙi a Hajjin 2025

Farfesa Abdullahi Saleh ya ƙara da cewa, yayin da masu zuwa Umrah ke biya da Naira, kamfanonin jiragen sama na dagewa kan sai an biya su Dala domin aikin Hajji, wanda hakan ke haifar da cikas ga ɗimbin maniyyata.

Kara karanta wannan

Akpabio: Shugaban majalisa ya gayawa Tinubu abin da za su yi wa kudirin haraji

Shugaban ya jaddada cewa magance wannan matsala zai haifar da raguwar kuɗin Hajjin shekarar 2025.

An mayarwa Alhazai kuɗaɗensu a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa Alhazan da suka yi aikin Hajji a shekarar 2023 sun samu kuɗaɗe daga hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Kano.

Hukumar ta ba mayar da N₦375,397,680 waɗanda ƙasar Saudiyya ta turo ga Alhazan guda 6,146 inda kowannensu ya samu N61,080.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng