Gwamna na Gina Katafariyar Makarantar Sheikh Dahiru Bauchi ta Farko

Gwamna na Gina Katafariyar Makarantar Sheikh Dahiru Bauchi ta Farko

  • An kaddamar da makarantar tunawa da Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda ake ganin ita ce irinta ta farko a Arewa maso Gabas
  • Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya ce za a gina irin makarantar a kowanne daga cikin kananan hukumomi 20 na jihar
  • Makarantar za ta magance matsalar yara marasa zuwa makaranta tare da samar da yanayi mai kyau domin karatu ga yara da malamai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Gwamnatin Jihar Bauchi ta fara gina makarantu na zamani domin bunkasa ilimi.

Gwamnan jihar, Sanata Bala Mohammed ya kaddamar da makarantar Sheikh Dahiru Usman Bauchi a Awala wanda aka bayyana a matsayin irinta ta farko a Arewa maso Gabas.

Makaranta
Ana gina makarantar tunawa da Sheikh Dahiru Bauchi. Hoto: Senator Bala Abdulqadir Mohammed
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda ake gina makarantar ne a cikin wani sako da Sanata Bala Mohammed ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

"Akwai lauje cikin nadi," Atiku ya zargi gwamnati da siyasantar da alkaluman NBS

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya bayyana cewa matakin wani bangare ne na shirin gina manyan makarantu a kowanne daga cikin kananan hukumomi 20 na jihar.

Tsarin makarantar Sheikh Dahiru Bauchi

Gwamnatin Bauchi ta ce za a tanadi kayayyakin zamani da za su ba yara damar karatu a yanayi mai kyau a makarantar tunawa da Sheikh Dahiru Usman.

Gwamnan ya ce makarantar za ta zama abin koyi a fannin ilimi, tare da kawo sauyi ga tsarin neman karatu a jihar Bauchi.

Yaki da rashin zuwa makaranta a jihar Bauchi

Gwamnatin Bauchi ta bayyana cewa makarantar tunawa da Sheikh Dahiru Usman Bauchi za ta kasance wata hanya ta magance matsalar yara marasa zuwa makaranta.

Sanata Bala Muhammad ya ce makarantar ba kawai za ta inganta ilimi ba ne, za ta bayar da dama ga dukkan yara wajen samun ilimi ba tare da nuna bambanci ba.

Gwamnan ya kara da cewa wannan aikin wata hanya ce ta kafa tubali mai karfi ga ci gaban ilimi da tattalin arziki a jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

An cafke fitaccen mawakin siyasa a Kano, an zargi yan Kwankwasiyya da hannu

Gwamnan Bauchi ya ba Tinubu shawara

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ba shugaban kasa Bola Tinubu shawarar cire tarkace cikin jami'an gwamnatinsa.

Gwamna Bala Mohammed ya ba Bola Tinubu shawarar ne a wani taron bude aiki da ya gudanar a jihar Rivers a makon da ya wuce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng