Yan Majalisa Sun Saka Ranar Raba Albashinsu ga Talakawan Najeriya

Yan Majalisa Sun Saka Ranar Raba Albashinsu ga Talakawan Najeriya

  • Majalisar Wakilai ta sanar da shirin miƙa gudummawar Naira miliyan 704.91 ga Shugaba Bola Tinubu domin taimakon talakawa
  • Gudummawar ta fito ne daga rabin albashin ‘yan majalisar na tsawon watanni shida da suka yi alkawari domin rage radadin rayuwa
  • Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen ya ce gudummawar za ta taimaka wajen magance matsalolin da talakawa ke fuskanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Majalisar Wakilai ta bayyana shirin miƙa gudummawar albashi da ta tara ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a ranar 31 ga Disamba, 2024.

Wannan matakin ya zo ne domin taimakawa masu rauni, musamman sakamakon tsadar rayuwa da cire tallafin man fetur ya haifar.

Bola Tinubu
Yan majalisa za su cika alkawarin raba albashi ga talakawa. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Jaridar Vanguarda ta wallafa cewa Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen ne zai jagoranci mika kudin ga Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Kwana 1 ga barazanar Turji, an yi kazamar fada tsakanin yan bindiga, an rasa rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'yan majalisa suka fara tara kudi

Mataimakin Shugaban Majalisar, Hon. Benjamin Kalu ne ya kawo kudirin tara kudin domin tallafawa talakawa a watan Yuli.

Tun a watan Yulin, ‘yan majalisar suka yanke shawarar cire rabin albashinsu na tsawon watanni shida domin tallafa wa talakawa, bayan amincewa da kudirin da Benjamin Kalu ya gabatar.

Yayin gabatar da kudirin, Bejamin Kalu ya ce:

"Gwamnatin nan tana ƙoƙarin gyaran kasa, amma shekara ɗaya ba za ta isa ba wajen magance matsalolin Najeriya.
"Ina roƙon abokan aiki na da mu sadaukar da kashi 50% na albashinmu na watanni shida ga talakawa.”

Za a mika albashin 'yan majalisa ga Tinubu

A yayin jawabi ga ‘yan majalisar a ranar Alhamis, Abbas Tajudeen ya ce:

“Mun yanke shawarar bayar da rabin albashinmu a matsayin gudummawa ga al’ummar Najeriya. Zuwa yanzu, mun tara Naira 704,907,578.82.”

Kara karanta wannan

Majalisa ta bukaci sakin shugaban Miyetti Allah, ta gayyaci hafsun tsaro

Punch ta wallafa cewa Abbas Tajudeen ya yaba wa ‘yan majalisar bisa jajircewarsu wajen kula da walwalar ‘yan Najeriya.

Ana ganin cika alkawarin rabon albashin ya nuna jajircewar ‘yan majalisar wajen taimakawa al’umma, musamman a wannan lokaci da ake fama da ƙalubalen tattalin arziki.

Kudirin haraji: An fara hada kan 'yan majalisa

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban majalisar wakilai ya fara lalubo hanyar tabbatar da kudirin harajin Bola Tinubu.

Rahotanni sun nuna cewa Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya fara neman hada kan 'yan majalisa ta bayan fage domin su amince da kudirin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng