Hukumar EFCC Ta Gayyaci Shugabannin Ƙananan Hukumomi 18 kan Zargin Kudi

Hukumar EFCC Ta Gayyaci Shugabannin Ƙananan Hukumomi 18 kan Zargin Kudi

  • Hukumar EFCC ta gayyaci ciyamomi 18 na kananan hukumomin jihar Edo da aka dakatar kan zargin almubazzaranci da dukiyar al'umma
  • EFCC ta sanya ranaku biyu da ciyamomin za su kawo kansu ofishinta domin amsa wasu tambayoyi kan zargin da ake masu
  • A wata wasiƙa da EFCC ta aikawa gwamnatin Edo, ta bukaci shugabannin su taho da wasu takardu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Edo - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gayyaci shugabannin kananan hukumomi 18 da aka dakatar a Edo zuwa ofishinta domin amsa tambayoyi.

Gayyatar na kunshe ne a cikin wata wasika da Daraktan bincike na EFFC, Abdulkarim Chukkol ya aikewa sakataren gwamnatin jihar Edo.

EFCC.
EFCC ta gayyaci shugabannin ƙananan hukumomin da aka dakatar a Edo Hoto: EFCC
Asali: UGC

Abdulkarim Chukkol, a cikin wasikar mai kwanan watan 17 ga Disamba, ya raba ranakun da ciyamomin za su kai kansu ofishin EFCC, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An cafke fitaccen mawakin siyasa a Kano, an zargi yan Kwankwasiyya da hannu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC ta aika sammaci ga ciyamomi 18

EFCC ta bukaci ciyamomin Akoko-Edo, Egor, Esan ta Tsakiya, Esan ta Arewa maso Gabas, Esan ta Kudu Maso Gabas, da Esan ta Yamma su kawo kansu ofis ranar Alhamus, 19 ga Disamba.

Sauran ciyamomin da ake sa ran za su halarci ofishin EFCC a ranar Alhamis sun hada da na kananan hukumomin Etsako ta tsakiya, Etsako ta Gabas, da Etsako ta Yamma.

Ragowar ciyamomin ƙananan hukumomi Igueben, Ikpoba Okha, Orhionmwon, Ovia North East, Ovia South West, Owan East, Owan West, da Uhunmwode, za su je ofishin EFCC ranar Juma'a.

Edo: EFCC ta bukaci su taho da takardu

Hukumar EFCC ta buƙaci ciyamomin su zo da kwafin takardun bayanan ma'aikatan da ke ƙarƙashin kananan hukumominsu da bayanan biyan albashi.

Sauran takardun da EFCC ta umarci ciyamomin su taho da su sun haɗa bayanan asusun da suke karɓar kason kuɗi da asusun da suke biyan ma'aikata albashi daga 1 ga Janairu zuwa yau.

Kara karanta wannan

'Ba ka isa ba': Ciyamomi 18 sun yi turjiya da Gwamna ya dakatar da su a jiharsa

Hukumar ta ce ta ɗauki wannan matakin ne dogaro da sashe na 38(1) (2) na kundik dokar kafa EFCC 2004, kamar yadda Punch ta rahoto.

Majalisa ta dakatar da ciyamomin Edo

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dokokin jihar Edo ta dakatar da ciyamomi 18 bayan sakon da ta samu daga gwamna Monday Okpebholo.

Gwamnan dai ya aika wasiƙa zuwa Majalisar yana gaya mata irin rashin ɗa'a da ladabin da shugabannin ƙananan hukumomin suka yi masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262