Birane da Gidaje: Gwamna a Arewa Ya Lashe Kyautar Gwarzon Shekara Ta 2024
- Gwamna Ahmed Aliyu ya zama gwarzon gwamnan da ya fi ba da gudummuwa a ɓangaren raya birane da gina gidaje a 2024
- An ba Ahmed Aliyu lambar yabo a wani biki da aka shirya a babban birnin tarayya Abuja bisa la'akari da ayyukan alherin da yake yi
- Mai magana da yawun gwamnan Sakkwato, Abubakar Bawa ya ce mai girma gwamna na kan aikin gina gidaje 1000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto - Gwamna Ahmed Aliyu na Sakkwato ya lashe lambar yabon gwarzon gwamnan da ya fi ba da gudummuwa a ɓangaren raya birane da gidaje na 2024.
Gwamna Aliyu ya lashe lambar yabon ne bayan karawa da gwamnoni uku da aka zaɓa don ba da kyauyar ta bana 2024.
Mai magana da yawun gwamnan Sakkwato, Abubakar Bawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Tribune Nigeria ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Aliyu ya zama gwarzon 2024
Ya ce an ba gwamnan lambar yabo ne bisa la’akari da irin kwazon da ya nuna wajen tsara birane da gina gidaj da kuma kawo tsarin samun takardar haƙƙin mallaka.
"Idan ba ku manta ba mai girma gwamma Ahmed Aliyu ya gina tare da ƙaddamar da tituna 30 a cikin gari, sannam ya gina tituna daban-daban guda 40 a manyan biranen Sakkwato.
“A tsarin samar da gidaje, yanzu haka Gwamna na gina gidaje 1000 a Gidan Salanke da Wajake, sannan ya sayi gidaje 137 da gwamnatin tarayya ta gina a unguwar Kwannawa."
"Wannan na cikin wani bangare na yunkurin mai girma gwamna wajen magance gibin gidaje da jama'ar jihar Sakkwato ke fuskanta.
Gwamnan Sokoto ya tura wakili Abuja
An bayar da lambar yabon ne ga Gwamna Ahmed Aliyu a wani gagarumin biki da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja.
Tsohon mataimakin gwamnan Sokoto, Chuso Abdullah Dajjijo ne ya karbi kyautar a madadin Gwamna Ahmed Aliyu.
Gwamna ya fara tallafawa nakasassu
Kuna da labarin gwamnan jihar Sakkwato ya fara biyan masu naƙasa alawus na N10,000 duk wata domin inganta rayuwarsu.
Bugu da ƙari, gwamnan ya raba keke guragu 500 da masu lalurar naƙasa duk a kokarin tallafa masu su yi rayuwa kamar kowa.
Asali: Legit.ng