Kano: Gobara Ta Kone Sashen Gidan Man NNPCL Kurmus, An Yi Asara

Kano: Gobara Ta Kone Sashen Gidan Man NNPCL Kurmus, An Yi Asara

  • Jama'a sun shiga zulumi bayan tashin wata mummunar gobara a gidan mai mallakin NNPCL da ke Kano
  • Lamarin ya faru da daddare a lokacin da wata mota dauke da fetur ke sauke mai a daren 17 Disamba, 2024
  • Hukumar kashe gobara ta Kano ta ce ana tsaka da sauke fetur din ne kwatsam, sai wuta ta tashi tare da jawo asara

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Jama'a da ke zaune kusa da gidan mai na NNPCL sun kidime bayan tashin gobara a gidan mai da ke makare da man fetur a lokacin.

Lamarin ya afku da 8.56 n.d a ranar Talata a gidan man NNPCL da ke titin Ibrahim Taiwo a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun rasu da taron murna ya turmutse a makarantar Musulunci

NNPCL
Gobara ta tashi a gidan man NNPCL Hoto: Saminu Yusuf Abdullahi
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, jami'in hulda da jama'a na hukumar kashe gobara, Saminu Yusuf Abdullahi ya tabbatar da lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an kwana-kwana sun kai gudunmawa NNPCL

SFS Saminu Yusuf Abdullahi ya tabbatar wa Legit afkuwar gobarar, wacce ta dauki ma'aikatanta daga ofisoshi daban-daban su ka yi nasarar shawo kanta.

Ya ce wani bawan Allah, Muhammad Abdullahi ne ya kira neman agajin jami'an hukumar, inda ya ce wuta ta kama ganga-ganga a gidan man NNPCL.

Abubuwan da su ka kone a NNPCL

Kafin jami'an hukumar kashe gobara ta Kano ta yi nasarar kashe gobarar, sai da aka tafka mummunan asara.

"Kan famfo na ba da kalanzir da kan famfo na ba da fetur guda biyu sun dan kone haka."
"Akwai motar dakon man fetur wacce ta ke mallakar kamfanin exchange energy, wacce ta ke dauke da man fetur kimanin lita 45,000 ta kama da wuta a yayin da ta ke sauke mai."

Kara karanta wannan

Yadda NNPCL ya karbo rancen dala biliyan 1 domin tallafawa matatar man Dangote

Ya ce motar ta sauke mai lita 32,000 zuwa ramin da ake ajiye fetur din kafin ta kama da wuta.

Matatar Fatakwal: NNPCL ya yi son kai

A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya sanar da wadanda matatar Fatakwal da aka gyara za ta rika sayar wa fetur da ake tacewa.

Babban jami’in sadarwa na kamfanin NNPCL, Olufemi Soneye, ya ce za a sayar da fetur da aka samar a matatar Fatakwal ga gidajen mansa a fadin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.