Yan Kasuwa Sun Sanar da Samun Saukin Farashin Litar Fetur
- Kungiyar MEMAN ta bayyana cewa farashin shigo da man fetur ya ragu daga watan Nuwamba zuwa Disambar 2024
- MEMAN ta bayyana cewa saukar farashin gangar danyen mai daga $74 zuwa $73.77 a kasuwar duniya ya jawo samun saukin
- Kungiyar ta ce sauka ko hawan farashin Dalar Amurka zai cigaba da shafar farashin danyen man fetur a kasuwannin duniya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar Manyan Dillalan Man Fetur ta Najeriya (MEMAN) ta bayyana cewa farashin dauko litar man fetur daga ketare ya ragu kaɗan.
Kungiyar MEMAN ta ce farashin litar mai ya ragu zuwa N970 a watan Disamba na 2024, idan aka kwatanta da N971 a watan Nuwamba.
Rahoton Vanguard ya nuna cewa duk da haka, wasu wuraren sayar da mai a Lagos ba su sauke farashin ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin saukar farashin mai a duniya
Bayanin da MEMAN ta yi ya nuna cewa raguwar farashin ya samu asali ne saboda saukar farashin gangar danyen mai zuwa $73.91.
Legit ta wallafa cewa kungiyar ta ce da sauyin Dala da Naira a kan N1,533.57/$ a kasuwar duniya ya yi tasiri a kan lamarin.
MEMAN ta kara da cewa tasirin siyasa da tattalin arziki, musamman lamuran Gabas ta Tsakiya, yanayin kasuwar kasar Sin, da sakamakon zaɓen Amurka za su iya tasiri a harkar mai a gaba.
Me ya hana farashin mai sauka a Najeriya?
A halin yanzu, farashin man fetur a Lagos bai sauka ba, farashin lita yana nan kan N1,025 a gidajen mai.
Shugaban Cibiyar Bunkasa Kasuwanci na Masu Zaman Kansu (CPPE), Dr Muda Yusuf ya bayyana cewa saukar farashin mai ba zai kasance da sauri ba saboda tsohon kaya da suke da shi a kasa.
Dangote ya rage farashin man fetur
A wani rahoton, mun ruwaito muku cewa matatar Dangote ta rage farashin man fetur ga 'yan Najeriya yayin da ake tsaka da tsadar rayuwa.
A sanarwar da matatar Dangote ta fitar, ta bayyana cewa za ta sayar da litar mai a kan N899 domin saukakawa mutane hidimar karshen shekara.
Asali: Legit.ng