Akpabio: Shugaban Majalisa Ya Gayawa Tinubu Abin da Za Su Yi Wa Kudiriin Haraji
- Shugaban majalisar dattawan Najeriya ya yabawa mai girma Bola Ahmed Tinubu kan kawo ƙudirin haraji da ake ta cece-kuce a kansa
- Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa majalisar tarayya ba za ta kashe ƙudirin ba wanda mutane da dama suka yi watsi da shi
- Ya bayyana cewa da ya daga cikin masu sukar ƙudirin ba su tsaya sun fahimce shi yadda ya kamata ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana cewa majalisar tarayyya ba za ta kashe ƙudirin haraji da ake ta cece-kuce a kai ba.
Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa masu sukar ƙudirin ba su fahimci abin da ya ƙunsa ba.
Shugaban majalisar dattawan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 da Shugaba Tinubu ya yi a zaman haɗin gwiwa na majalisar tarayya jiya a Abuja, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Akpabio ya gayawa Tinubu kan haraji?
Sanata Godswill Akpabio ya ce ba zai yiwu a kashe wannan “daftarin doka mai kyau” ba, rahoton Channels tv ya tabbatar.
Ƙudurorin dai sun sha caccaka inda wasu gwamnoni, ƴan majalisar tarayya, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin farar hula (CSOs) da sauran ƴan Najeriya da dama suka yi watsi da su.
"Mai girma shugaban ƙasa, muna yaba maka kan shirin sake fasalin haraji."
"Abin takaici ne cewa waɗanda ba su ɗauki lokaci ba domin fahimtar waɗannan ƙuɗirorin su ne suka fi suka."
"Ina kira ga ɗaukacin ƴan Najeriya, musamman waɗanda ke riƙe da mukaman gwamnati, da su tsaya su fahimci waɗannan ƙudirorin masu amfani cikin natsuwa."
"Ba za mu kashe duk wani ƙudirin sake fasali da ka gabatar mana domin nazari a kansa ba, amma za mu tattauna da ƴan Najeriya domin su ga amfaninsu."
- Sanata Godswill Akpabio
Tinubu ya yi barkwanci a majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi suɓul da baka a gaban ƴan majalisar tarayya yayin gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025.
Bayan an yi masa gyara kan kuskuren da ya yi, Shugaba Tinubu ya maida abin barkwanci wanda hakan ya jawo shewa daga wajen ƴan majalisar.
Asali: Legit.ng