"Yesu ba Allah ba Ne," Wata Bana da Aka Liƙa a Babban Masallaci Ta Tayar da Ƙura
- Babban Masallacin Lekki a jihar Legas ya haifar da cece-kuce bayan liƙa wata bana mai isar da saƙon cewa Yesu ba Allah ba ne
- Mutane da dama sun maida martani kan banar da ke yawo a kafafen sada zumunta, wasu na ganin gaskiya ne wasu kuma na ganin saɓo ne
- Rubutun da ke cikin banar ya nuna cewa 'Jesus' da Kiristoci ke bauta wa ba Allah ba ne, bawan Allah ne kuma manzonsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Wata bana da aka liƙa a kofar shiga babban masallacin Lekki da ke jihar Legas ta haifar da kace-nace a shafukan sada zumunta.
A jikin banar Masallacin wanda ta yadu a ranar Laraba, an rubuta, “Yesu Kiristi ba Allah ba ne. Shi Annabi ne kuma Manzon Allah!"

Asali: Twitter
Yadda banar ta haifar da mahawa mai zafi

Kara karanta wannan
Karyar ƴan bindiga da sauran miyagu ta kare a Najeriya, sanata ya hango shirin Tinubu
Saƙon da ke cikin banar ya girgiza intanet, inda ƴan Najeriya suka yi zazzafar mahawara kan shi, wasu na ganin saƙon ba ƙaramin saɓo ba ne, Vanguard ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yesu dai shi ne Annabi Isa A.S da mabiya addinin kirista ke bauta wa, a ɗaya ɓangaren Musulmai na girmama shi a matsayin ɗaya daga cikin Manzannin Allah SWT.
Wasu daga cikin masu amfani da soshiyal midiya sun nuna damuwa kan sakon banar, sun ce ɓatanci ne yayin da wasu suka gaskata rubutun da ke jiki.
A gefe guda kuma, wasu tsirarun mutane sun kare wannan rubutu, inda suka bayyana cewa a baya limaman coci da kansu sun tabbatar da haka.
Martani wasu ƴan Najeriya kan banar
Wata jarumar fim a Najeriya, Wumi Tuase ta nuna rashin jin dadin ta da wannan bana, inda ta ce:
"Ban cika son tsoma baki a taƙaddamar addini ba amma na ji wani iri da babban Masallacin Lekki ya liƙa wannan a ƙofar shiga."
@Dannymasterp ya maida martani da cewa:
"Babu shakka Yesu ba Allah ba ne kuma hujja a bayyane take, majami'u sun fi maida hankali wajen bayyana mu'ujizozinsa maimakon koyarwarsa."
"Suna kiransa Allah ne saboda yana yin mu’ujizozi ba tare da sanin hakan wata hanya ce ta sa mutane su gaskata shi ɗan aiken Allah ne ba."
@shinoremy ya ce:
"Gaskiya ne ko karya ne ba shi ne abin dubawa a rubutun banar ba, sai dai an yi haka ne da manufar sukar wani addini.
"Kuma kasancewar daga Musulmai ya fito zai iya haifar da rikicin addini, ya kamata mu rika mutunta juna."
Gwamnatin Legas ta rufe cocin RCCG
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Legas ta rufe wata cocin RCCG da otal-otal kan zargin saɓawa dokar sauti da hayaniya
Hukumar kula da mahalli ta jihar Legas ta ce babu wani shafaffe da mai da zai take doka kuma gwamnati ya kyale shi, dole ne ta ɗauƙi mataki.
Asali: Legit.ng