Mutane da Dama Sun Rasu da Taron Murna Ya Turmutse a Makarantar Musulunci

Mutane da Dama Sun Rasu da Taron Murna Ya Turmutse a Makarantar Musulunci

  • Hargitsi ya kashe rayuka a taron sada zumunci da aka gudanar a makarantar Musulunci ta Basorun a Ibadan.
  • Gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya ce an dauki matakan gaggawa domin shawo kan lamarin, ciki har da tura jami’an tsaro
  • Gwamnatin jihar Oo ta tabbatar da cewa masu shirya taron sun shiga hannun hukuma yayin da bincike ke ci gaba da gudana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Oyo - Hatsarin yamutsi da ya faru a makarantar Musulunci ta Basorun a Ibadan ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da raunata wasu.

Lamari ya jefa jihar Oyo cikin jimami, yayin da gwamna Seyi Makinde ya bayyana alhini tare da daukar matakan shawo kan lamarin.

Makinde
Yamutsi ya kashe mutane a jihar Oyo. Hoto: Seyi Makinde
Asali: Twitter

Legit ta gano halin da aka shiga ne a cikin wani sako da gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Jerin abubuwa 6 da gwamnatin Tinubu za ta yi wa 'yan Najeriya a shekarar 2025

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakin da aka dauka bayan turmutsi

Gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya bayyana cewa gwamnati ta tura jami’an tsaro zuwa wurin domin dawo da doka da oda, yayin da aka dakatar da taron gaba daya.

Rahoton Channels ya nuna cewa an aike da ma’aikatan lafiya da motocin daukar marasa lafiya zuwa wurin domin kula da wadanda suka samu raunuka.

A cewar Makinde, gwamnati ta tabbatar da cewa ba za a sake samun rasa rayuka ba a wurin, sannan an dauki matakan tabbatar da tsaron wurin.

Masu shirya taron tun shiga hannu

Gwamnan ya ce wadanda suka shirya taron da ya haifar da hatsarin turmutsitsin sun shiga hannun jami’an tsaro.

SEyi Makinde ya kuma tabbatar wa da al’ummar jihar cewa za a dauki matakan hukunta duk wanda aka samu da hannu kai tsaye ko a kaikaice a lamarin.

Gwamna Makinde ya yi ta'aziyya

Kara karanta wannan

Belin N500m: Kotu ta saki belin Yahaya Bello, an kafa masa sharuda masu tsauri

Gwamna Makinde ya jajantawa iyalan wadanda hatsarin ya rutsa da su, yana ma addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bin doka da oda tare da bayar da hadin kai ga jami’an tsaro wajen binciken abin takaicin.

Za a yi karin albashi a jihar Oyo

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya yi alkawarin fara biyan ma'aikata sabon mafi karancin albashi a sabuwar shekara.

Gwamna Seyi Makinde ya yi alkawarin biyan ma'aikatan jihar N80,000 a watan Janairu mai kamawa domin su samu damar walwala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng