Daga Karshe Gwamna Abba Ya Fadi Dalilin Yin Zazzaga a Gwamnatinsa
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi magana kan surutun da ake yi sakamakon garambawul da ya yi a gwamnatinsa
- Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa babu siyasa a cikin garambawul ɗin ya yi wanda ya shafi wasu a majalisar zartaswar jihar
- Gwamnan ya bayyana cewa zai sake dawo da waɗands aka raba da muƙamansu a cikin gwamnati a nan gaba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi magana kan garambawul da ya yi wa majalisar zartaswa ta jihar.
Gwamna Abba ya yi watsi da batun cewa akwai siyasa a cikin korar da ya yi wa shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, sakataren gwamnatin jiha da kwamishinoni biyar.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakinsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba ya bayani kan korar da ya yi
Gwamnan wanda ya yi magana a wajen taron majalisar zartaswar jihar a ranar Laraba, ya yi watsi da batun cewa an sanya siyasa a cikin garambawul ɗin da ya yi.
Gwamna Abba Kabir ya bayyana cewa gwamnati ta ɗauki matakin ne da zuciya ɗaya da kuma duba maslahar Kano.
"A ƴan kwanakin nan mun yanke wasu hukunce-hukunce a gwamnati, ciki har da yin garambawul a majalisar zartaswa."
"Sakamakon wannan mataki wasu sun rasa muƙamansu, wasu kuma an sauya musu wurin aiki. Bari na tunatar da jama’a cewa matakin da aka ɗauka, an yi ne domin maslahar mutanen Kano."
- Abba Kabir Yusuf
Meyasa Gwamna Abba ya yi garambawul?
A cikin sanarwar, Gwamna Abba ya jaddada cewa buƙatar sauke wasu kwamishinonin, ta zama tilas ne domin kawo sabon jini waɗanda za su taimaka wajen cimma manufofin gwamnati.
Gwamnan ya bayyana cewa waɗanda suka rasa muƙaman na su, za a sake shigo da su cikin gwamnati.
"Bari kuma na bayyana cewa ba wai mun rabu da su ba kenan gaba ɗaya, muna da wasu ayyukan da za mu ba su, domin haka ina son kowa ya karɓi matakin a yadda ya zo."
- Abba Kabir Yusuf
Majalisa ta tabbatar da kwamishinonin Abba
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dokokin jihar Kano ta tantance sababbin kwamishinonin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa.
Majalisar dokokin ta tabbatar da naɗin da gwamnan ya yi wa mutum bakwai domin zama kwamishinoni a gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng