An Taso Dan Takarar Shugaban Kasa a Gaba kan Sukar Buhari a Ranar Haihuwarsa
- Omoyele Sowore ya tunzura wasu ƴan Najeriya kan kalaman da ya yi a kan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya yi kalamai masu kaushi a kan Buhari inda ya zarge shi da lalata ƙasar nan
- Sai dai, kalaman da Sowore ya yi a kan Buhari, sun jawo masa suka daga wasu ƴan Najeriya waɗanda ba su ji daɗinsu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan Najeriya, Omoyele Sowore, ya caccaki Muhammadu Buhari.
Omoyele Sowore ya ƙi bin sahun masu aika saƙon fatan alheri ga tsohon shugaban ƙasan yayin da ya cika shekara 82 a duniya, a ranar Talata, 17 ga watan Disamban 2024.
A wani rubutu da ya yi a shafinsa na X, Sowore ya zargi Muhammadu Buhari da lalata ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane da dama sun taya Buhari murnar cikarsa shekara 82 a duniya tare da yi masa fatan alheri.
Me Sowore ya ce kan Buhari?
Sowore ya bayyana cewa bai kamata Buhari ya samu wata karramawa, yabo ko farin ciki ba saboda lalata ƙasar nan da ya yi.
"Mutumin da ya lalata ƙasarsa bai cancanci samun kowace irin karramawa, lambar yabo ko farin ciki ba"
"Baba munafikin banza. Baba barawa banza."
An dura kan Sowore saboda sukar Buhari
Ƴan Najeriya da dama sun yi wa Omoyele Sowore martani kan kalaman da ya yi a kan Muhammadu Buhari.
Da yawa daga ciki sun caccake shi kan rashin ganin girman tsohon shugaban ƙasan da ya yi.
Ga wasu daga ciki:
@Qladele:
"Kuma kana son ka tsufa. Ina tausayin rayuwarka."
@Hausatechguy:
"Ba za ka taɓa mulkar ƙasar nan ba"
@OfficialEdoOsasB
"Kana zagin mai gidanka domin bai baka muƙami ba? SoWerey!
@mustyO:
"Ubanka ne ɓarawo"
@AabalarabeMnim:
"Saidai bakin ciki yalasheka sowore marar tarbiyya banza"
@suleiman_qasim:
"Lokacin da ya ke gwamna, kakanka yana can yana ɗiban manja a ƙauyenku."
"Lokacin da yake minista, kakanka ya haifi banzan babanka"
"Lokacin da yake shugaban ƙasa, banzan babanka ya auri mamarka sannan suka haifi sakaran yaro"
"A matsayinka na sakaran yaro, shugaban ƙasan ka ne har sau biyu!"
"Dan kutuma ubanka matsayaci, tsinanne! Allah ya TSINE maka Hege"
Atiku ya taya Buhari murnar cika shekara 82
A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar ya taya tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, murnar cika shekara a duniya.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya yi addu'ar fatan samun tsawancin kwana cikin ƙoshin lafiya ga Muhammadu Buhari.
Asali: Legit.ng