Gwamna Ya Shirya Yin Afuwa ga Masu Garkuwa da Mutane da Sauran Laifuffuka

Gwamna Ya Shirya Yin Afuwa ga Masu Garkuwa da Mutane da Sauran Laifuffuka

  • Gwamnan jihar Anambra ya shirya ɗaukar matakan da yake ganin za su taimaka wajen magance masa matsalar rashin tsaro
  • Charles Chukuwma Soludo zai iya yin afuwa ga masu garkuwa da mutane, ƴan fashi da makami da sauransu waɗanda suka tuba
  • Duk masu son yin amfani da wannan damar domin ajiye makamansu, suna da daga nan har zuwa ƙarshen watan Fabrairun 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Anambra - Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, ya yi alƙawarin yin afuwa ga masu aikata laifuka da suka tuba.

Gwamna Soludo ya yi alƙawarin yin afuwar ne ga masu garkuwa da mutane, ƴan ƙungiyar asiri, masu safarar miyagun kwayoyi, ƴan fashi da makami, masu satar motoci, masu yankan aljihu da sauran su a jihar.

Soludo zai yi wa masu laifuka afuwa a Anambra
Gwamna Soludo zai yiwa masu garkuwa da mutane afuwa a Anambra Hoto: Prof. Charles Chukwuma Soludo
Asali: Facebook

Soludo ya yi wannan alƙawarin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamna da ke Amawbia a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

Gwamna zai yafewa 'dan shekara 17 da kotu ta yankewa hukuncin kisa saboda satar zabo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Soludo ya yi magana ne kan halin da ake ciki na rashin tsaro a jihar, musamman yayin da ake tunkarar bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara da ke tafe.

Gwamna Soludo zai yi wa masu laifi afuwa

Ya ce gwamnatinsa ta shirya tsaf domin yin afuwa ga duk wani mai laifi da ke son miƙa kansa da makamansa cikin lumana, rahoton Daily Post ya tabbatar.

"Gwamnatina za ta tabbatar da cewa irin waɗannan mutane sun samu gyaran tarbiyya, da kuma ba su damar zama ƴan ƙasa masu amfani a cikin al’umma."
"Duk masu son yin amfani da wannan damar, to su yi rajista da ofishin mai ba gwamna shawara kan harkokin tsaro, kuma wannan ƙofar za ta ci gaba da kasancewa a buɗe har zuwa ƙarshen watan Fabrairun 2025."

- Gwamna Chukwuma Soludo

Gwamna Soludo ya fara biyan sabon albashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Anambra ƙarƙashin jagorancin Gwamna Chukwuma Soludo, ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata.

Kara karanta wannan

Yaki da 'yan bindiga: Manyan Arewa sun halarci kaddamar da askarawa 5,000

Gwamnatin ta fara biyan sabon albashin na N70,000 domin inganta walwala da jin daɗin ma'aikatan da suke aiki a ƙarƙashinta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng