Uba Sani Ya Faranta Ran Iyalan Abacha, Ya Mayar da Abin da Aka Kwace a Lokacin El Rufai

Uba Sani Ya Faranta Ran Iyalan Abacha, Ya Mayar da Abin da Aka Kwace a Lokacin El Rufai

  • Gwamnan jihar Kaduna ya mayarwa iyalan Sani Abacha filayen da aka ƙwace musu a lokacin gwamnatin Nasir El-Rufai
  • Uba Sani ya mayar da filayen ne guda biyu ga iyalan tsohon shugaban ƙasan na mulkin soja bayan an ƙwace su a shekarar 2022
  • Lauyan iyalan Abacha ya yaba da matakin mayar da filayen da ke a cikin birnin Kaduna, inda ya bayyana hakan a matsayin gaskiya da adalci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya mayarwa iyalan tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Sani Abacha, wasu filaye biyu da aka ƙwace musu a baya.

Gwamna Uba Sani ya mayar da filayen ne ga iyalan Abacha bayan an ƙwace su a lokacin gwamnatin Malam Nasir El-Rufai.

Uba Sani ya mayar da filaye ga iyalan Abacha
Uba Sani sauya matakin El-Rufai kan filayen iyalan Abacha Hoto: @ubasanius, @elrufai
Asali: Twitter

Uba Sani ya sauya matakin El-Rufai

Jaridar The Punch ta ce filayen waɗanda ke a No.9 Abakpa GRA da No.1 Degel Road, Ungwan Rimi GRA, a cikin garin Kaduna, an kwace su ne a shekarar 2022 sakamakon zargin karya sharuɗɗan dokar amfani da filaye.

Kara karanta wannan

Abba ya nada kwamishioni 6, hadimin da aka tsige zai dawo gwamnatin Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana a ranar Talata, lauyan iyalan Abacha, Reuben Atabo (SAN), ya tabbatar da mayar da filayen, yana mai bayyana hakan a matsayin wani gagarumin ci gaba, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.

Atabo ya ce matakin ƙwace filayen ya haifar da “abin kunya” ga iyalan Abacha, lamarin da ya sa suka ɗauki matakin shari'a a kan gwamnatin jihar.

Wane sharaɗi aka kafawa iyalan Abacha?

Gwamna Uba Sani, ya sauya matakin ƙwace filayen ne a wasu wasiƙu daban-daban guda biyu masu ɗauke da kwanan wata 10 ga watan Disamba, 2024, ta hannun hukumar KADGIS.

Wasiƙun biyu, waɗanda Mustapha Haruna ya sanyawa hannu a madadin babban daraktan KADGIS, sun umurci iyalan da su biya kuɗaden da aka biyo su a matsayin sharaɗin dawo musu da filayen.

Iyalan Abacha, ta bakin Atabo, sun yi maraba da matakin, inda suka bayyana shi a matsayin nuna gaskiya da adalci.

Uba Sani ya ba da muƙami

Kara karanta wannan

Yaki da 'yan bindiga: Manyan Arewa sun halarci kaddamar da askarawa 5,000

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, ya naɗa mai ba shi shawara na musamman kan harkokin ƙananan hukumomi.

Gwamna Uba Sani ya damƙa wannan sabon muƙamin a hannun tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kachia, Kabiru Yakubu Jarimi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng