Gwamnati Ta Bankado Ma'aikatan Bogi Masu Karbar Albashin N3.6bn

Gwamnati Ta Bankado Ma'aikatan Bogi Masu Karbar Albashin N3.6bn

  • Gwamnatin jihar Jigawa na ci gaba da aikin tantance ma'aikata domin gano na bogi masu karɓar albashi ba bisa ƙa'ida ba
  • A aikin tantancewar, gwamnatin Jigawa bankaɗo ma'aikatan bogi guda 6,348 da ke samun kuɗaɗe ba tare da gudanar da aiki ba
  • Kwamishinan yaɗa labarai, matasa da wasanni na jihar Jigawa, Sagir Musa, ya ce gwamnatin ta rage kashe N3.6bn a shekara sakamakon gano ma'aikatan na bogi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ta bankaɗo ma’aikatan bogi 6,348 da ke karɓar albashi.

Gwamnatin jihar Jigawan ta gano ma'aikatan na bogi ne a aikin tantancewa da take gudanarwa.

Gwamnatin Jigawa ta gano ma'aikatan bogi
Gwamnatin Jigawa ta bankado ma'aikatan bogi Hoto: @aunamadi (X)
Asali: Twitter

Mista Sagir Musa, kwamishinan yaɗa labarai, matasa, wasanni da al’adu, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a birnin Dutse, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: An shiga jimami bayan 'yar NYSC ta fadi ta mutu a sansanin horaswa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano ma'aikatan bogi a Jigawa

Ya ce rahoton aikin tantance ma’aikatan jihar baki ɗaya da aka fitar, ya nuna cewa an gano ma’aikatan bogi guda 6,348.

Kwamishinan yaɗa labaran ya bayyana cewa gano ma'aikatan bogin ya ba gwamnatin jihar damar rage kashe sama da Naira miliyan 314 duk wata.

Sagir Musa ya ce majalisar zartaswar jihar ta yi nazari kan rahoton kuma ta amince da kafa cibiyar ci gaba da tantancewa (CCC) a ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati.

"Aikin tantancewar ya haifar da gano ma’aikatan bogi guda 6,348 kuma an rage kashe kuɗaɗe masu yawa na N314,657,342.06 a kowane wata da kuma N3,775,888,809.72 a shekara."

- Sagir Musa

Gwamnatin Jigawa ta yi wa ma'aikata gata

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa ta shirya tallafawa ma'aikata bayan amincewa da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.

Gwamnatin ta kawo tsarin da jami'an lafiya za su samu gata kamar yadda takwarorinsu da ke aiki a ƙarƙashun gwamnatin tarayya suke samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng