Shugaba Tinubu Ya Taya Buhari Murnar Cika Shekara 82, Ya Yi Masa Yabo

Shugaba Tinubu Ya Taya Buhari Murnar Cika Shekara 82, Ya Yi Masa Yabo

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bi sahun masu taya Muhammadu Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa
  • Mai girma Bola Tinubu ya miƙa na sa saƙon taya murnar cika shekara 82 a duniya da tsohon shugaban ƙasan ya yi
  • Mai girma Shugaba Tinubu ya yaba da ayyukan da Buhari ya yi da kuma jajircewarsa wajen kawo ci gaba a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya miƙa sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwar Muhammadu Buhari wanda ya cika shekaru 82 a duniya.

Shugaba Tinubu ya yaba da irin gudunmawar da tsohon shugaban ƙasan ya bayar wajen ci gaban Najeriya.

Tinubu ya taya Buhari murnar cika shekara 82
Shugaba Tinubu ya taya Muhammadu Buhari murnar cika shekara 82 a duniya Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Bola Tinubu ya yabawa Muhammadu Buhari

Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da hidimin shugaban ƙasa, Dada Olusegun, ya sanya a shafinsa na X a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Atiku ya manta da siyasa, ya tura sako mai muhimmanci ga Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya yaba da jajircewar Buhari, ya bayyana shi a matsayin shugaba wanda jajircewarsa ta kawo ci gaba a Najeriya.

Tinubu ya yabawa tsohon shugaban ƙasan bisa jagorancinsa a matsayinsa na shugaba na farko a gwamnatin APC a Najeriya.

Ya sha alwashin ci gaba da ɗorawa kan ayyukan more rayuwa da Buhari ya yi a lokacin mulkinsa.

Tinubu ya taya Buhari murnar cika shekara 82

"A madadin gwamnati da al’ummar Najeriya ina miƙa sakon taya murna da fatan alheri a gare ka kan cika shekara 82 da haihuwa."
"A wannan rana ta musamman, ina maka fatan samun ƙauna daga wajen ƴan uwa da abokai, da ci gaba da samun ƙoshin lafiya, farin ciki da gamsuwa dukkanin harkokinka, a yanzu da kuma nan gaba."
"Barka da zagayowar ranar haihuwa, muna godiya bisa ayyukan da ka yi wa Najeriya. Tare da girmamawa da jinjinawa."

- Shugaba Bola Tinubu

Atiku ya taya Buhari murna

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin shugaban kasa ya caccaki Obasanjo a sakon taya Buhari murna

A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar, ya aika da saƙon taya murnar zagayowar ranar haihuwa ga Muhammadu Buhari a yau.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya ya taya shi murna, ya yi masa addu'ar samun tsawancin kwana cikin ƙoshin lafiya da kuzari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel