Bola Tinubu Ya Gana da Zababben Shugaban Ghana, Sun Tattauna Batutuwa a Abuja

Bola Tinubu Ya Gana da Zababben Shugaban Ghana, Sun Tattauna Batutuwa a Abuja

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da zaɓaɓɓen shugaban kasar Ghana, John Mahama a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja
  • Mista John Mahama ya kawo ziyara Najeriya ne kwanaki bayan ya lashen zaben shugaban Ghana da aka gudanar
  • Tuni dai shugaban Najeriya ya taya shi murnar lashe zaɓen da ya ba shi damar komawa kan mulki bayan shekaru takwas

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya karɓi bakuncin zaɓaɓɓen shugaban kasar Ghana, John Mahama a fadarsa da ke Abuja.

John Mahama ya kawo wa Bola Tinubu ziyara ne kwanaki kaɗan bayan lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar da kasar Ghana.

John Mahama da Bola Tinubu.
zababben shugaban Ghana, John Mahama ya ziyarci Bola Tinubu a Abuja Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Wannan nasara dai ta ba Mahama damar komawa kan karagar mulki shekaru takwas bayan ya mulki kasar Ghana.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya naɗa Aisha Garba a babban muƙamin gwamnatin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zababben shugaban Ghana ya ziyarci Tinubu

Mai taimakawa shugaban Najeriya kan harkokin kafafen sada zumuntar zamani, Olusegun Dada ne ya tabbatar da ziyarar John Mahama a shafinsa na X.

Hadimin Tinubu ya ce:

“Zababben shugaban kasar Ghana, Mai girma John Dramani Mahama ya kai wa shugaba Tinubu ziyarar ban girma a gidansa da ke fadar shugaban kasa jiya."

Sai dai Olusegun Dada bai yi wani ƙarin bayani ko abubuwan da shugabannin biyu suka tattauna a wannan ziyara ta jiya Litinin ba.

Kimanin kwanaki goma da suka gabata, Tinubu ya aika da sakon taya murna ga Mahama bayan nasarar da ya samu a zaben shugaban ƙasar Ghana.

Mahama ya samu nasara a zaɓen Ghana

John Mahama ya mulki Ghana tsakanin 2012 zuwa 2016 kuma a bana watau 2024 ya sake samun nasarar komawa kan madafun iko.

Ya samu nasarar doke Mahamudu Bawumia, mataimakin shugaban kasar mai ci bayan ya samu kashi 56.55% na kuri'un da aka kada.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Tinubu ya dawo da zancen kudirin haraji, ya cigaba da lallabar jama'a

Mataimakin shugaban Ghana ya samu kashi 41.6 na ƙuri'un da aka kaɗa kuma tuni ya amince da shan kaye a hannun abokin hamayyarsa.

Bola Tinubu ya naɗa shugabar UBEC

A wani labarin, kun ji cewa Bola Tinubu ya naɗa Aisha Garba a matsayin wacce za ta jagoranci hukumar kula da ilimin bai ɗaya ta Najeriya watau UBEC.

Shugaban kasar ya ce yana fatan za ta kawo sauyi a harkokin ilimin yaran Najeriya ta yadda za a fafata da su a duniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262