Gwamna Zai Raba Tallafin Naira Biliyan 3.9, Za a ba Jama'a Katin Cire Kudi

Gwamna Zai Raba Tallafin Naira Biliyan 3.9, Za a ba Jama'a Katin Cire Kudi

  • Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya ware sama da Naira biliyan 3.9 domin tallafawa al'umma
  • Za a raba tallafi a yankuna 65, manoma 19,068, da kananan 'yan kasuwa 4,095 domin bunkasa tattalin arzikin jihar
  • Shirin ya tallafa wa mutane sama da miliyan 1.9 a zagayen da ya gabata tare da inganta rayuwar al'umma a Katsina

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya kaddamar da zagaye na hudu na shirin KT-CARES a filin wasa na Malumfashi.

Shirin ya kunshi raba tallafi na sama da Naira biliyan 3.9 domin inganta rayuwar al'umma ta hanyar ayyukan ci gaba da tallafi ga marasa galihu.

Dikko Radda
Dikko Radda ya kaddamar da raba tallafin N3.9bn. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Source: Facebook

Hadimin gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa yadda rabon tallafin zai gudana a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Matar Tinubu ta shigo Arewa ta raba miliyoyin Naira a jihohi

A karkashin shirin, gwamnan ya bayyana cewa za a tallafa wa yankuna 65 da kudi tsakanin Naira miliyan 2 zuwa miliyan 11 domin gudanar da ayyuka masu amfani da suka zaba da kansu.

Mutanen da za a tallafawa a Katsina

Gwamna Radda ya sanar da cewa mutane 3,600 za su samu katunan ATM domin samun tallafin rage radadin rayuwa.

Kananan 'yan kasuwa 4,095 za su karbi tallafi tsakanin Naira 100,000 zuwa Naira 500,000 domin bunkasa sana'o'insu.

Haka kuma, manoma 19,068 za su samu kayan aikin noma da suka hada da injunan ban ruwa na sola, 'ya'yan kifi, kaji, da sauran kayayyaki domin inganta harkar noma.

Karin bayani kan shirin KT-CARES

Gwamna Radda ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kashe fiye da Naira biliyan 9.2 a zagaye uku na baya na shirin KT-CARES wanda ya tallafa wa sama da mutane miliyan 1.9.

Kara karanta wannan

Kama tsofaffin gwamnoni, ministoci da manyan nasarorin EFCC da ICPC a shekarar 2024

Shirin ya kunshi raba kayan aikin noma ga manoma 23,800 da kuma bayar da tallafi ga kananan 'yan kasuwa 3,835 domin bunkasa kasuwancinsu.

Radda ya jaddada cewa an umurci jami'an KT-CARES su gudanar da tsare-tsaren sa-ido da tantancewa domin tabbatar da cewa an cimma manufar shirin.

Gwamna Radda ya raba mukamai

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda PhD ya gwangwaje masu mutane da mukamai a gwamnati.

Legit ta wallafa cewa gwamna Dikko Umaru Radda ya naɗa sabon kwamishina da shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Katsina.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng