Majalisar Dokokin Kano Ta Fadi Matsayarta kan Kwamishinonin da Gwamna Abba Ya Nada
- Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da sunayen mutanen da aka tura mata domin zama kwamishinoni
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ne ya tura sunayen mutanen guda bakwai ga majalisar shiga gwamnatinsa
- Majalisar dokokin ta tabbatar da mutanen ne bayan ta kwashe tsawon sa'o'i uku da rabi ana tantance su a ranar Talata
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da sunayen mutane bakwai da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa domin tantancewa su zama kwamishinoni.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa sunayen ne domin tantance su a matsayin mambobin majalisar zartaswa ta jihar.
Jaridar The Punch ta rahoto cewa majalisar ta tabbatar da mutanen ne a yayin zamanta na ranar Talata, 17 ga watan Disamban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa ta tabbatar da kwamishinonin Abba
Tabbatar da su ta biyo bayan ɗaukar sa’o’i uku da rabi ana tantance mutanen da aka naɗa domin zama kwamishinoni, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.
Daga nan majalisar ta yi amincewar bai ɗaya domin zama kwamishinoni a gwamnatin Gwamna Abba.
Da yake sanar da hakan a yayin zaman, shugaban majalisar, Jibril Falgore, ya bayyana cewa tabbatar da su ya biyo bayan amincewa da ƙudirin hakan da ƴan majalisar suka yi.
Waɗanda aka tabbatar sun haɗa da tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano, Shehu Wada Sagaji, wanda aka sauke shi daga muƙaminsa tare da sakataren gwamnatin jihar (SSG), Dr. Abdullahi Baffa Bichi.
Sauran kwamishinonin da aka tabbatar sun haɗa da Abdulkadir Abdulsalam, Gaddafi Sani Shehu, Ibrahim Wayya, Dr. Dahiru Hashim Muhammad.
Sannan akwai Dr. Ismail Aliyu Dannaraya da Kwamred Nura Iro Maaji da aka aika sunansa daga baya.
Gwamna Abba ya yi sababbin naɗe-naɗe
A wani labarin kuma, kun ji cewa rabo ya ratsa kan wasu yayin da gwamnan jijar Kano, ya amince da yin sababbin naɗe-naɗe a gwamnatinsa.
Gwamna Abba ya naɗa sababbin masu ba shi shawara na musamman tare da shugabannin wasu hukumomin gwamnatin jihar.
Daga cikin waɗanda suka samu muƙaman har da fitaccen jarumi a masana'antar Kannywood, Sani Musa Danja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng