Atiku Ya Manta da Siyasa, Ya Tura Sako Mai Muhimmanci ga Buhari
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya taya tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari murnar cika shekara 82 a duniya
- A cikin saƙon taya Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa, Atiku ya yi fatan Allah ya ƙarawa tsohon shugaban ƙasan tsawon rai cikin ƙoshin lafiya da kuzari
- Tsohon shugaban ƙasan wanda ya ba da gudunmawa ga ci gaban Najeriya, ya cika shekara 82 a duniya a ranar Talata, 17 ga watan Disamban 2024
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya aika da saƙon taya murna ga tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Atiku Abubakar ya aika da saƙon taya murnar ne ga Muhammadu Buhari yayin da ya cika shekara 82 a duniya a ranar Talata, 17 ga watan Disamban 2024.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, ya taya Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa ne a wani rubutu a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya yi wa Buhari addu'a
A saƙonsa na murnar zagayowar ranar haihuwar Buhari, Atiku ya yi addu’ar Allah ya ƙarawa tsohon shugaban ƙasan tsawon kwana cikin ƙoshin lafiya da kuzari.
"A madadin iyalaina ina taya tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari @MBuhari murnar cika shekara 82 a duniya. Ina addu'ar Allah ya ƙara maka shekaru cikin ƙoshin lafiya da kuzari."
- Atiku Abubakar
Buhari ya cika shekara 82 a duniya
Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya cika shekaru 82 a ranar Talata,17 ga watan Disamba, 2024.
Buhari wanda aka haifa a ranar 17 ga watan Disamba, 1942, ya taka rawa a fagen soja da siyasa, inda ya zama shugaban ƙasa a mulkin soja da na farar hula
Hadimin Buhari ya cacccaki Obasanjo
A wani labarin kuma, kun ji cewa Garba Shehu wanda shi ne tsohon mai magana da yawun bakin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya caccaki Olusegun Obasanjo.
Garba Shehu ya yi shaguɓe ne ga tsohon shugaban ƙasan a saƙon taya Muhammadu Buhari murnar cika shekara 82 a duniya.
Asali: Legit.ng