Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci kan Rikicin Sarauta, Ta Hana Gwamna Naɗa Sabon Sarki
- Babbar kotun jihar Osun ta dakatar da gwamna, kwamishina da Antoni Janar daga naɗa sabon Owa-Obokun na Ijesa Land
- Mai shari'a Adeyinka Aderibigbe ya ba da umarnin dakatar da shirin naɗa sabon sarkin a wata kara da ƴan gidan Ofokutu suka shigar
- A watan Satumba, 2024, Mai martaba Oba Gabriel Aromolaran ya mutu bayan shafe shekaru 42 a kan gadon mulkin kasar Ojesa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun - Babbar kotun jihar Osun mai zama a Ilesa ta dakatar da Gwamna Ademola Adeleke daga naɗa sarkin masarautar Ijesa land.
Kotu ta dakatar da Adeleke, kwamishinoni da wasu masu ruwa da tsaki daga naɗa Yarima Clement Adesuyi a matsayin sarkin Ijesa Landa watau Owa-Obokun.
The Nation ta tattaro cewa Yarima Clemet ya fito daga gidan sarautar Haastrup kuma babbar kotu ta haɗa naɗa shi ko wani yarima a sarautar Owa-Obokum na ƙasar Ijesa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta tsoma baki a rikicin sarautar Ijesa
Idan ba ku manta ba sarkin Ijesa Land, Oba Gabriel Aromolaran ya mutu a watan Satumba, 2024 bayan shafe shekaru 42 a kan gadon sarauta.
Bayan rasuwarsa, ƴan gidan sarautar da dama suka nuna sha'awar zama magajin sarkin, hakan ya sa masu alhakin naɗa sarki suka fara shirin tantancewa.
Yayin da ake shirye-shiryen naɗa sarki, babbar kotun Osun ta ba da umarnin wucin gadi na hana naɗin magajin Oba Gabriel Aromolaran.
Mai shari'a Adeyinka Aderibigbe ya ba da umarnin hana Gwamna Adeleke, kwamishinan kananan hukumomi da masarautu da Antoni-Janar naɗa sabon Owa-Obokun.
Dalilin hana gwamna naɗa sabon Owa-Obokum
Alkalin ya bayar da umarnin ne biyo bayan bukatar da Yarima Debo Adeyemi, Prince Adeboye Adewale, da wasu mutane tara na gidan sarautar Ofokutu suka gabatar.
Sun bukaci kotun da ta dakatar da duk wani shirin naɗa sabon sarkin ciki har da karbar Naira miliyan 10 daga hannun masu neman sarautar.
Bayan amincewa da bukatarsu, Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Junairu, 2025.
Sarki daga Kudu ya ziyarci Muhammadu Buhari
A wani labarin, kun ji cewa Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura a jihar Katsina.
Basaraken ya bayyana cewa Buhari ya yi iya bakin kokarinsa a tsawon shekaru takwas da ya shafe a kan mulkin Najeriya daga Mayun 2015 zuwa 2023.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng