Tsohon Hadimin Shugaban Kasa Ya Caccaki Obasanjo a Sakon Taya Buhari Murna
- Tsohon mai magana da yawun Muhammadu Buhari, ya caccaki tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo
- Malam Garba Shehu ya soki Olusegun Obasanjo kan yadda yake caccakar shugabannin ƙasan da suka biyo bayansa
- A ɗaya ɓangaren kuma, Garba Shehu ya yabawa Buhari kan yadda ya ƙauracewa Abuja tun bayan da ya bar mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Garba Shehu tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya caccaki tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo.
Garba Shehu ya caccaki Obasanjo ne a saƙon taya murnar zagayowar ranar haihuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari wanda ya cika shekara 82 a yau.
Garba Shehu ya taya Buhari murnar cika shekara 82 a duniya ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Garba Shehu ya caccaki Obasanjo
Garba Shehu ya caccaki Obasanjo kan yadda ya yake sukar shugabannin da suka biyo bayansa.
Tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasan ya kuma ya yabawa Buhari, kan ƙauracewa Abuja domin ba sabuwar gwamnati damar gudanar da tsare-tsarenta.
"A ɗaya ɓangaren kuma, tun bayan da ya bar mulki, na farko a mulkin soji, da zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasa bayan wa’adi biyu, Olusegun Obasanjo ya riƙa rubuta wasiƙa ga duk wani shugaban ƙasa a bayansa domin ya kunyata su."
"A wasu lokutan ma har yana neman su yi murabus ko kiran ka da a sake zaɓensu a zaɓe mai zuwa."
- Garba Shehu
Garba Shehu ya yabi Buhari
Garba Shehu ya kuma bayyana cewa tun bayan kammala wa’adinsa a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, sau biyu kacal Buhari ya ziyarci babban birnin tarayya Abuja.
Ya ce Buhari ya cika alƙawarinsa na barin sabuwar gwamnati ta yi aiki ba tare da yi mata katsalandan ba.
Garba Shehu ya ƙara da cewa a yanzu Buhari yana yin sauƙaƙƙiyar rayuwa, wanda ya haɗa da zama da jikokinsa, ganawa da baƙi, duba gonarsa, tare da yin karatu da kallon shirye-shiryen talabijin.
Gwamnonin Arewa sun taya Buhari murna
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya sun taya Muhammadu Buhari murnar cika shekara 82 a duniya.
Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya bayyana tsohon shugaban ƙasan a matsayin jajirtaccen shugaba kuma abin koyi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng