Nazarin Karshen Shekara: Manyan 'Yan Siyasa Mata 6 da Suka Taka Rawa a 2024
FCT, Abuja - A shekarar 2024, mata ƴan siyasa da dama a Najeriya sun taka rawar gani wajen jagoranci da nasarorin da suka samu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Waɗannan matan ba wai kawai sun zama kallabi tsakanin rawuna ba ne, har ma sun zaburar da mutane da dama kan yadda suke sadaukarwa wajen aikin gwamnati da gudanar da mulki.
Legit Hausa ta haska jiga-jigan ƴan siyasa mata da suka taka rawar gani a Najeriya a 2024:
Matan da suka yi fice a siyasa a 2024
1. Oluremi Tinubu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Oluremi Tinubu, uwargidan shugaban ƙasa Bola Tinubu ta yi fice a fagen siyasar Najeriya.
Ta taka muhimmiyar rawa wajen shirye-shiryen bunƙasa walwalar jama'a, da yin kira wajen kare haƙƙin mata da samar musu da sana'o'i.
Tasirin ta ya zarce matsayinta na uwargidan shugaban ƙasa, a baya ta taɓa zama uwargidan gwamnan jihar Legas da kuma sanata mai wakiltar Legas ta Tsakiya.
2. Ireti Heebah Kingibe
Ireti Heebah Kingibe, ƴar jam’iyyar LP, ta samu kujerar sanata mai wakiltar babban birnin tarayya Abuja a zaɓen 2023.
Ireti Kingibe wacce ta shahara wajen samar da ci gaba da inganta rayuwar al’umma, ta sha yin takun saƙa da ministan Abuja kan wasu tsare-tsarensa.
3. Uju Kennedy Ohanenye
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Uju Kennedy Ohanenye a matsayin ministar harkokin mata a watan Agustan 2023 kuma ya maye gurbinta a 2024, cewar rahoton tashar Channels tv.
Ta yi suna wajen nemawa mata haƙƙinsu, inda a lokacin da take minista ta sha tsayawa tsayin daka wajen ganin an ƙwatowa matan da aka ci zarafinsu haƙƙoƙinsu.
A matsayinta na lauya, ƴar kasuwa, kuma mai shirya fina-finai, ta kafa tarihi a matsayin mace ta ɗaya tilo da ta tsaya takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC a zaɓen 2023.
4. Erhiatake Ibori-Suenu
Erhiatake Ibori-Suenu, wacce tsohuwar ƴar jam'iyyar PDP ce, ta yi tasiri sosai a siyasar jihar Delta.
Erhiatake Ibori Suenu da ke wakiltar mazaɓar Ethiope a majalisar wakilai, kwanan nan ta sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.
A matsayinta na ɗiyar tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori, tana jajircewa wajen ganin ta kawo ci gaba ga mutanen da take wakilta.
5. Hannatu Musa Musawa
Hannatu Musa Musawa, wadda aka naɗa ministar fasaha, al'adu, da tattalin arziƙin fikira, ta yi suna a matsayin lauya, ƴar siyasa, kuma marubuciya.
Gudunmawar da ta bayar a ɓangaren al’adu ya taimaka sosai wajen tallata al’adun gargajiyar Najeriya.
6. Natasha Akpoti
Sanata Natasha Hadiza Akpoti lauya ce, ƴar kasuwa kuma ƴar siyasa da ta taka rawar gani a bana.
Ita ce wadda ta kafa wani shiri mai suna Builders Hub Impact Investment Program (BHIIP), wanda ke mayar da hankali kan samar da ayyukan yi ta hanyar farfaɗo da masana'antun cikin gida na Najeriya.
Sanata Natasha Akpoti ta yi suna ne bayan fallasa cin hanci da rashawa a kamfanin sarrafa tama da ƙarafa na Ajaokuta.
Jaridar Vanguarɗ ta rahoto cewa sanatar ta buƙaci majalisar dattawa ta binciki yadda ake gudanar da kamfanin tun daga shekarar 2008 zuwa yanzu.
Ireti Kingibe ta fice daga majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatan da ke wakiltar birnin tarayya Abuja a majalisar dattawa, Ireti Kingibe, ta nuna fushinta a zauren majalisar.
Sanatar ta fice daga zauren majalisar dattawan bayan bayan Sanata Godswill Akpabio ya daƙile ta daga gabatar da ƙudirinta kan rusau da Nyesom Wike yake yi a birnin Abuja.
Ireti Kingibe dai tana adawa ne da yadda ministan birnin Abuja, ke yin rushe-rushe babu ƙaƙƙautawa wanda hakan ya shafi mutane da dama ta hanyar raba su da matsugunansu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng