"Ku Ƙara Imani da Allah SWT," Gwamna Ya Yi Magana bayan Gobara Ta Laƙume Miliyoyin Naira

"Ku Ƙara Imani da Allah SWT," Gwamna Ya Yi Magana bayan Gobara Ta Laƙume Miliyoyin Naira

  • Gobara ta lakume dukiyoyi na Miliyoyin Naira a kasuwar Gwari da ke Minna, babban birnin jihar Neja ranar Litinin da yamma
  • Gwamna Mohammed Umaru Bago ya jajantawa ƴan kasuwar da lamarin ya shafa, ya bukaci su ƙara imani da Allah SWT
  • Ya ce gwamnatinsa za ta agaza masu domin rage raɗaɗin asarar da suka yi, ya kuma koka kan karuwar tashin gobara a Minna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Gobara ta lalata kayayaki na miliyoyin Naira a babbar kasuwar Gwari da ke Minna, babban birnin jihar Neja.

Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne a bangaren dillalan kasuwar a ranar Litinin da yamma kafin ta yaɗu zuwa wasu sassa.

Gwamnan Neja, Umar Bago.
Gwamna Bago ya jajantawa waɗanda ibtila'in gobara ya shafa a Minna Hoto: Mohammed Umaru Bago
Asali: Facebook

A rahoton Daily Trust, shaidu sun ce an dauki sa’o’i da dama kafin a shawo kan gobarar saboda rashin samun hanyoyin shiga kasuwar.

Kara karanta wannan

"Dole sai na tantance" Gwamna ya shinfida sharaɗin fara biyan albashin N80,000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Bago ya jajantawa ƴan kasuwa

Gwamna Umaru Bago ya jajantawa waɗanda ibtila'in gobarar ya shafa a wata sanarwa da sakataren watsa labaransa, Bologi Ibrahim ya fitar a Minna, Channels tv ta rahoto.

Umar Bago ya ce ibtila'in gobarar abin takaici ne kuma wata jarabawa ce ga waɗanda ta rutsa da su, inda ya kara da cewa shi kansa bai ji daɗin lamarin ba.

Bago ya kuma ja hankalin ƴan kasuwar da lamarin ya shafa su miƙa lamarinsu ga Allah kuma su kara imani da Shi domin zai iya miada masu fiye da abin da suka rasa.

Gwamna ya nuna damuwa kan ƙaruwar gobara

Ya kuma nuna damuwa kan yawaitar tashin gobara a wurare daban-daban a jihar Neja musamman kwaryar birni watau Binna.

Sakamakon haka, Gwamna Bago ya bukaci hukumomin da ke da alhaki su wayar da kan jama'a domin daƙile yawaitar tashin gobara da ke jawo asarar kadarori.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Mata da miji sun rasu ta hanya mai ban tausayi a jihar Kano

Daga ƙarshe, Umaru Bago ya tabbatar wa ƴan kasuwar da gobara ta shafa cewa gwamnati za ta agaza masu domin rage raɗaɗin asarar da suka yi.

Bago ya yi ta'aziyyar rasuwar ciyaman

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Bago ya yi ta'aziyyar rasuwar shugaban ƙaramar hukumar Katcha ta jihar Neja, Ɗanlami Abdullahi Saku.

Mai girma Umar Bago ya yi nasiha ga sauran al'umma cewa ya kamata wannan rasuwa ta tuna masu da cewa kowace rai za ta ɗanɗana ɗacin mutuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel