Majalisa Ta Amince a Kashe Biliyoyi a Gina Tashoshin Lantarki a Sokoto da Wasu Garuruwa

Majalisa Ta Amince a Kashe Biliyoyi a Gina Tashoshin Lantarki a Sokoto da Wasu Garuruwa

  • Gwamnatin tarayya ta yi wa 'yan kasar nan albishir da samar da wasu tashoshin wutar lantarki a sassan daban-daban
  • Ministan da ke kula da harkokin wutar lantarki, Adebayo Adelabu da ya tabbatar da haka, ya ce za a kashe biliyoyi a harkar
  • Ya shaida cewa garuruwan da za su amfana da gagarumin aikin sun hada da Sakkwato sai Onitsha da Abeokuta da ke Kudu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Majalisar zartarwa ta kasa (FEC) ta bayar da damar kashe biliyoyin Naira domin magance matsalolin wutar lantarki a sassan kasar nan hudu.

Ministan harkokin lantarki, Adebayo Adelabu ne ya tabbatar da matakin yayin da ‘yan kasa ke kuka da matsalar karancin hasken wuta.

Kara karanta wannan

Kama tsofaffin gwamnoni, ministoci da manyan nasarorin EFCC da ICPC a shekarar 2024

Lantarki
Za a samar da tashoshin wutar lantarki a garuruwa hudu Hoto: Adebayo Adelabu, Transmission Company of Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa za tuni aka bayar da kwangilar gagarumin aikin ga kamfanin Siemens da ke kasar Jamus don aiwatar da aikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a samar da tashoshin wutar lantarki

Jaridar Businessday ta wallafa cewa Naira biliyan N262.75 domin gina tashoshin wutar lantarki a garuruwa guda hudu da ke sassan kasar nan.

Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce za a gina sababbin cibiyoyin lantarki masu ƙarfin 330/132 KV da kuma 132/33 KV a wuraren guda biyar.

Garuruwan da za su amfana da tashar lantarki

Majalisar zartawar kasar nan ta amince da samar da tashoshin wutar lantarki a biranen Sakkwato da Onitsha da Abeokuta da offa da kuma Ayede.

Adebayo Adelabu, ya ce aikin ya hada da gine-gine da sayen na’urori da kuma hada su, wanda aka ba wa kamfanin Siemens na ƙasar Jamus kwangila.

Wutar lantarki: Najeriya na aiki da Jamus

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin kasar nan ta tabbatar da cewa ta sanya hannu a kan yarjejeniya da kamfanin Jamus domin kakkabe matsalar lantarki.

Kara karanta wannan

An cafke masu lalata turakan lantarki a Najeriya suna kokarin tafka barna

Ministan da ke kula da harkokin makamashi, Adebayo Adelabu, ya ce akwai dangantaka mai a tsakanin kasashen tun bayan amincewa da wata yarjejeniya ta shekarar 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.