"Dole Sai Na Tantance," Gwamna Ya Shinfida Sharaɗin Fara Biyan Albashin N80,000
- Gwamnan Akwa Ibom ya ce ba zai fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N80,000 ba sai an kammala tantance ma'aikata
- Fasto Umo Eno ya ce babu wata barazana da ƴan kwadago za su yi masa da zai sa ya tsallake tsarin da ya ɗauko kafin ƙarin albashi
- Gwamna ya kuma sanar da cewa zai ba ma'aikata albashin watan 13 saboda su yi shagulgulan kirismeti cikin walwala
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Akwa Ibom - Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya gindaya sharaɗi ga ma'aikata kafin fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N80,000.
Gwamna Eno ya jaddada cewa ba zai fara aiwatar da dokar sabon albashin ba har sai an kammala tantance ma'aikatan gwamnatin Akwa Ibom gaba ɗaya.
Gwamna ya gindaya sharaɗin biyan N80,000
Gwamnan ya ce babu wata barazanar yajin aiki daga kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) da za ta tilasta masa fasa wannan tsari, Daily Trust ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fasto Umo Eno ya bayyana haka ne a wurin taron fara bukukuwan kirismeti na jiha karo na 17 wanda ya gudana a Uyo.
Gwamna Eno ya kuma bai wa ma’aikatan gwamnati tabbacin cewa zai gwangwaje su da albashin wata 13 domin su yi shagalin kirismeti.
Ya yi bayanin cewa za a lissafa ƙarin kudin da za a ba kowane ma'aikaci ne bisa tsarin albashin da ake da shi, har sai an kammala aikin tantancewa, in ji Vanguard.
Gwamnan Akwa Ibom zai biya albashin wata 13
"A matsayain gwaamnanku zan biya albashin watan 13, mun riga mun gama lissafi kuma za mu biya ne bisa tsohon tsarin albashi.
"Ba zamu fara aiwatar ɗa sabon mafi karancin albashi ba har sai an kammala aikin tantance ma'aikata.
"Babu wanda zai tilasta ni na fara biya ba tare da gama tantancewa ba, da zarar NLC, wacce ke cikin kwamitin tantancewa ta kawo rahoto za mu fara biyan kudi nan take."
- Gwamna Eno.
NLC ta hakura da shiga yajin aiki
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar NLC ta janye yajin aikin da ta shirya a jigar Akwa Ibom bayan gwamna ya amince da sabon albashin N80,000.
A cewar shugaban NLC na reshen jihar, gwamnan Akwa Ibom ya amince zai fara aiwatar da sabon albashin a karshen watan Disamba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng