Kashim Shettima Ya Sauka a Saudiyya, Zai Yi Ayyuka 2 kafin Dawowa Gida

Kashim Shettima Ya Sauka a Saudiyya, Zai Yi Ayyuka 2 kafin Dawowa Gida

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya karasa kasar Saudiyya a ziyarar aiki da ya kai kasashen larabawa biyu
  • Kashim Shettima ya fara zuwa Dubai, inda aka kaddamar da katafariyar cibiyar adana mai mallakin kamfanin Najeriya
  • Ana sa ran mataimakin shugaban kasar zai dawo gida Najeriya bayan ya yi ganawa ta musamman da mahukuntan Saudi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Saudia - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya isa Saudiyya domin gudanar da wasu muhimman ayyuka guda biyu kafin dawo wa Najeriya.

Mataimakin shugaban kasar ya sauka a filin jirgin sama na Mohammad Bin Abdulaziz da ke Madina, Saudiyya, a ranar Litinin.

Kashim
Mataimakin shugaban kasa ya sauka a Saudiyya Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Wannan na kunshe ne a cikin sakon da mai baiwa Kashim Shettima shawara kan yada labarai, Stanley Nkwocha, ya fitar a shafin X a yammacin ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Abba ya nada kwamishioni 6, hadimin da aka tsige zai dawo gwamnatin Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami’an Saudiyya sun tarbi Kashim Shettima

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa da isarsa Saudiyya mataimakin gwamnan yankin Madina, Abdulmohsen Bin Nayef Bin Hamed ya tarbe shi.

Sauran wadanda su ka tari mataimakin shugaban sun hada da jami’an diflomasiyyar Najeriya ciki har da jakadan Najeriya a Jeddah, Ambasada Mu’azzam Nayaya.

Ayyukan da Kashim Shettima zai gudanar a Saudi

Mataimakin shugaban kasar yana ziyara a Madina domin ibadar umrah a Madina da Makkah domin kara kusanci da Allah SWT.

A ranar 20 ga watan Disamba, 2024 kuma Sanat Shettima zai yi taro na musamman da Shugaban Bankin Raya Kasashen Musulmi (IsDB) a Jeddah a kasa mai tsarki.

Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan shirin hadin gwiwa na kudi domin bunkasa yankunan sarrafa kayayyakin noma da sauran batutuwa.

Kashim Shettima ya ziyarci Dubai

A wani labarin, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ziyarci Dubai da ke hadaddiyar Daular Larabawa domin wakiltar shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen kaddamar da aiki.

Kara karanta wannan

Badenoch: Igboho ya bukaci Tinubu ya ja kunnen Shettima kan sukar Bayarbiya

Kashim Shettima zai halarci kaddamar da wata cibiyar adama man fetur mallakin kamfani dan asalin Najeriya, 'Oriental Energy Limited' wanda kimarsa ya kai akalla Dala miliyan 315.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.