Atiku Ya Buɗe Shafin da Ƴan Najeriya Za Su Samu Tallafin N65,000? Hadiminsa Ya Yi Bayani

Atiku Ya Buɗe Shafin da Ƴan Najeriya Za Su Samu Tallafin N65,000? Hadiminsa Ya Yi Bayani

  • Atiku Abubakar ya nesanta kansa da wani shirin tallafi da ake yaɗawa cewa shi ne zai rabawa ƴan Najeriya kyautar N65,000
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ba shi da alaƙa da shafin yanar gizo na tallafin, ya bukaci mutane su kaucewa sharrin ƴan damfara
  • Kakakin Wazirin Adamawa, Paul Ibe ya ce da alamu ƴan damfara ne suka kirkiro shirin tallafin domin yaudarar ƴan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya nesanta kansa da wani shirin tallafi da ke yawo da sunansa a kafofin sada zumunta.

Atiku, ɗan takarar PDP a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ya gargaɗi ƴan Najeriya su gujewa shirin wanda aka yi ikirarin ba duk wanda ya cancanta tallafin N65,000.

Atiku Abubakar.
Atiku ya gargaɗi yan Najeriya su kaucewa faɗawa hannun yan damfara da sunan tallafi daga wurinsa Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Mai magana da yawun Wazirin Adamawa, Paul Ibe ne ya bayyana hakan a a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X ranar Litinin.

Kara karanta wannan

"Ban da karba karba": Shekarau ya fadi hanyar samar da shugaban kasa a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya bullo da shirin tallafawa ƴan Najeriya?

A ƴan kwanakin nan dai, mutane na ta yaɗa wani shafin yanar gizo tare da ikirarin cewa Atiku Abubakar zai ba da tallafin N65,000 ga duk wanda ya cika sharuɗɗa.

Shafin na kunshe da wani fom da ake bukatar duk wanda zai nemi tallafin ya cike suna, lambar asusu da sunan banki.

Amma a sanarwar, Paul Ibe ya ce Atiku ba shi da alaƙa da shafin kuma babu wani shiri da ya ɓullo da shi a yanzu na bai wa ƴan Najeriya tallafin kudi.

Atiku Abubakar ya gargaɗi ƴan Najeriya

Bisa haka ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike domin gano masu hannu a wannan shirin tallafi na damfara.

"Mai girma tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar PDP a 2023, Atiku Abubakar bai ɓullo da wani shirin ba mutane tallafin N65,000 ba a yanzu."

Kara karanta wannan

An samu asarar rayuka bayan jirgin ruwa ya kife da fasinjoji a jihar Arewa

"Shirin da ake yaɗawa na 'Atiku Grant by FG' damfara ce da aka kirkiro da nufin sace kuɗaden da ƴan Najeriya suka nema da guminsu, muna kira ga mutane su guji tsarin."

- Paul Ibe.

Atiku ya tallafawa ɗalibai a Adamawa

Rahoto ya gabata cewa Atiku ya bullo da wani shirin tallafawa ɗaliban da suka fito daga gidajen talakawa a jiharsa watau Adamawa.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya rabawa ɗaliban wasu makarantu kusan 20 kayan karatu, sannan ya ɗauki nauyin karatun wasu daga cikin ɗaliban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262