Hafsan Sojoji Ya Fadi Hanyar Kawo Karshen 'Yan Ta'addan Lakurawa

Hafsan Sojoji Ya Fadi Hanyar Kawo Karshen 'Yan Ta'addan Lakurawa

  • Babban hafsan sojoji ƙasan Najeriya (COAS), Laftanar Janar Olufemi Olatunbosun Oluyede ya taɓo batun ƴan ta'addan Lakurawa
  • Hafsan sojojin ya bayyana cewa jami'an tsaro na ƙara zafafa kai hare-hare kan ƴan ta'addan da ke a yankin Arewa maso Yamma
  • Laftanar Janar Oluyede ya nua cewa sojojin Najeriya a shirye suke su kawar da duk wata barazana ga tsaron ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Babban hafsan sojojin ƙasa (COAS), Laftanar Janar Olufemi Olatunbosun Oluyede, ya yi magana kan ƙoƙarin da ake yi domin kawar da ƴan ta'addan Lakurawa.

Laftanar Janar Oluyede ya bayyana cewa ana ci gaba da zafafa yaƙin da ake yi da ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa a yankin Arewa maso Yamma.

Hafsan sojoji ya magantu kan 'yan ta'addan Lakurawa
Hafsan sojoji ya ce ana kokarin fatattakar 'yan Lakurawa Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Hafsan sojojin ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron shekara-shekara na COAS na 2024 da aka gudanar a hedkwatar rundunar da ke Abuja, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi galaba kan 'yan bindiga, sun ceto mutanen da suka sace

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji na ragargazar ƴan ta'addan Lakurawa

Laftanar Janar Oluyede ya tabbatarwa ƴan Najeriya ƙudirin Sojoji na kawar da barazana ga tsaron ƙasa.

Hafsan sojojin ya bayyana cewa sojojin da ake aiki a atisayen Operation Fansan Yamma, sun ƙara zage damtse wajen kawar da ayyukan ta’addancin Lakurawa.

"Ana ci gaba da ƙara samun bayanan sirri, tura dakaru na musamman, hare-hare ta sama da ƙasa domin kawar da duk wata barazana a yankin."
"Bugu da ƙari, ana yin aiki tare da mutanen ƙauyaku domin samun bayanai da ƙarin haɗin kai wajen tunkarar ƴan Lakurawa da sauran ƙungiyoyin ta'addanci."

- Laftanar Janar Olufemi Olatunbosun Oluyede

Hafsan sojojin ya nuna muhimmancin tsarin yin amfani da ƙarfin soji da dabaru domin tabbatar da ɗauwamammen zaman lafiya da tsaro a yankunan da matsalar tsaro ta shafa.

Sojoji sun cafke shugaban ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke wani shugaban ƴan ta'adda kuma dillalin makamai mai suna Bako Wurgi.

Sojojin na runduna ta ɗaya sun cafke ɗan ta'addan wanda ake zargin yana da hannu a kisan da aka yi wa Sarkin Gobir a Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng