Gwamnoni Sun Shiga Alhini, Sun Yi Ta'aziyyar Mutuwar Mutane a Hadarin Jirgin Binuwai

Gwamnoni Sun Shiga Alhini, Sun Yi Ta'aziyyar Mutuwar Mutane a Hadarin Jirgin Binuwai

  • Gwamnonin kasar nan sun bayyana alhinin yadda aka tafka asarar rayuka a jihar Binuwai sakamakon hadarin jirgin ruwa
  • Gwamnan jihar Kwara kuma shugaban kungiyar NGF, AbdulRahman AbdulRazaq a madadin takwarorinsa ya yi ta'aziyya
  • Ya bayar da shawarwari ga hukumomi domin daukar matakan da za su dakile yawan hadurra, musamman na jirgin ruwa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Benue - Kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta mika ta’aziyyarta ga al’ummar Biuwai da gwamnatin jihar kan rasuwar mutane 20.

Mutanen sun rasa rayukansu ne sakamakon hatsarin jirgin ruwa da ya faru a karshen makon da ya gabata a karamar hukumar Agatu ta jihar.

Gwamnati
Gwamnonin Arewa sun mika ta'aziyya ga Binuwai Hoto: Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

TVC news ta wallafa cewa sakon alhinin na kunshe a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara ya sa wa hannu.

Kara karanta wannan

Abba ya nada kwamishioni 6, hadimin da aka tsige zai dawo gwamnatin Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin jihohi sun yi ta’aziyyar mutanen Binuwai

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kungiyar gwamnonin kasar nan ta yi fatan Allah SWT ya ji kan mutanen da su ka rasu rayukansu a hadarin jigin ruwan Binuwai.

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce;

“Mun mika ta’aziyyarmu ga mai girma gwamna Rev. Fr. Hyacinth Alia da al’ummar jihar kan wannan mummunan al’amari. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya ji kan wadanda suka rasa rayukansu.”

Gwamnoni sun ba da shawara kan hadurra

Gwamnonin kasar nan sun shawarci hukumomin da ke da alhakin kula da harkokin sufuri su kara himma wajen tabbatar da doka da oda domin hana irin wadannan hadurra.

Sun kara da yin kira ga jama’a da masu aikin jiragen ruwa su guji tafiye-tafiye a dare, yin lodin da ya wuce kima, da kuma bin dukkan dokokin tsaro a kowane lokaci.

Kungiyar NGF ta kara da cewa;

"Kungiyar gwamnoni ta kuma yabawa masu bayar da agajin gaggawa da suka ceto mutane 11 daga cikin fasinjojin da suka tsira da ransu."

Kara karanta wannan

Kwana 1 da korar na Kano, wani sakataren gwamnatin jiha ya ajiye aikinsa a Arewa

Fetur: Gwamnoni sun gayyaci NNPCL

A wani labarin, kun ji cewa gwamnonin kasar nan sun fusata biyo bayan yadda Najeriya ke ci gaba da sayo man fetur daga kasashen waje, duk da tarin albarkar danyen manta.

Gwamnonin sun kuma bayyana mamakinsu a kan matsalolin man fetur da ake fama da shi a kasar nan, duk da cewa Najeriya na daga cikin manyan 'yan kungiyar OPEC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel